Daga Khalid Idris Doya,
Masu garkuwa da mutane sun sace Babban Limamin Cocin Katolika mai mukamin Bishop, Most Rabaran Dakta Moses Chikwe.
Masu satar mutanen sun yi awon gaba da malamin cocin ne ranar Lahadi a garin Owerri tare da direbansa.
Rundunar ‘yan sandan jihar Imo ta jaddada cewa ta baza jami’anta domin ganin an ceto Rabaran din mai shekara 53.
Kakakin ‘yan sandan jihar, SP Orlando ikeokwu, ya ce sashen yaki da masu garkuwa da mutane na rundunar karkashin jagorancin CSP Linus Nwalwu ya bazama domin kama miyagun.
“Mu na neman mutane da su kwantar da hankulansu a irin wannan yanayi maras dadi,” in ji shi.
Jami’in yana mai cewa hukumarsu a shirye take wajen cigaba da yin kokarinta domin tabbatar da kare rayuka da dukiyar jama’a, ya bada tabbacin rundunar na ceto wanda aka yi garkuwa da shi.