A wani al’amari mai tayar da hankali a Jihar Sokoto, Sarkin Gobir na Gatawa, Alhaji Isa Muhammad Bawa, tare da ɗan sa da wasu mutane biyar sun shiga hannun ƴan bindiga a hanyar Sokoto-Sabon Birni.
Masu garkuwa da mutanen sun nemi kuɗin fansa har Naira biliyan daya domin sakin su. Kakakin rundunar ƴan sandan jihar Sokoto, ASP Ahmed Rufa’i, ya tabbatar da faruwar lamarin, inda ya ce jami’an tsaro na gudanar da bincike kan lamarin.
- Xie Yu Ya Lashe Lambar Zinare A Wasan Harbin Karamar Bindiga Daga Nisan Mita 10 Ajin Maza A Gasar Olympics Ta Paris
- CDD Ta Soki NBC Kan Cin Tarar Trust TV Da Wasu Miliyan 20
Alhaji Isa Gobir, wani ɗan Sarkin Gobir ɗin da aka yi garkuwa da shi, ya bayyana cewa harin ya faru ne a kwanar Maharba yayin da suke tafiya daga Sokoto zuwa Sabon Birni.
Ƴan bindigan sun buɗe wuta kan motar Sarkin, inda suka huda tayoyin motar, wanda hakan ya jawo direban ya rasa iko da motar, suka tsaya cak. Ƴan bindigan suka yi awon gaba da Sarkin da direbansa, wanda shi ma ɗan sa ne. Gobir ya yi kira ga gwamnati da ta dauki matakin gaggawa domin ceto mahaifinsa da sauran wadanda aka yi garkuwa da su. Wannan garkuwar ta jawo fushi da damuwa mai yawa a tsakanin mazauna Sabon Birni.
Al’ummar suna roƙon hukumomi da su ɗauki mataki cikin gaggawa domin tabbatar da dawowar Sarkin yankin da sauran waɗanda aka sace cikin koshin lafiya.