BBC ta rawaito cewa, Jami’an tsaro da ‘yan banga sun yi nasarar kubutar da mutanen nan da ‘yan bindiga suka yi garkuwa da su a ranar Alhamis, a kauyen Gujinduguri da ke yankin karamar hukumar Alkaleri a jihar Bauchi.
Mutanen da adadinsu ya kai talatin sun sami ‘yancinsu ne, bayan wani samamen hadin gwiwa tsakanin ‘yan sanda da ‘yan banga, wanda ya kai ga fafatawa da ‘yan bindigar.
- ‘Yansanda Sun Cafke Dalibai 3, Da Wani Bisa Zargin Shiga Kungiyar Asiri A Bauchi
- Makiyayi Ya Datse Hannun Manomi A Bauchi
Cindo Muhammad Gujinduguri, na cikin wadanda aka ceto ‘yan’uwansu, ya shaida cewa ba bu wani da aka bari a cikin wadanda aka yi garkuwa da su:
“ Gaskiya iya mutanen da aka tafi da su, ba bu guda daya wanda aka ba shi a baya, duk an kwatosu an dawo da su”, in ji shi.
Cindo Muhammed Gujinduguri ya ce ba bu kudin fansa da aka biya wajan ceto mutanen, a cewarsa farmakin da jami’an tsaro tare da hadin gwiwar ‘yan banga suka kai wa mabuyar ‘yan bindigar ne ya kai ga cetosu.
“ Jami’an tsaro ne kawai suka shiga da ‘yan banga, su ka je su ka karbesu, kuma jama’a da dama ne suka fito dominsu tarbesu”, in ji shi.
A cikin mutum 30 da ‘yan bindigar suka yi garkuwa da su akwai mata da kananan yara da maza.
Yankin na Gujinduguri na cikin yankunan da ke fama da tashin hankali a karamar hukumar Alkaleri da ke jihar Bauchi.
Mazauna yankin sun ce ‘yan bindigar sun tare hanya inda suka yi awon gaba da mutanen da ke cikin motocci da kuma babura wanda su ka ci kasuwar Mararraba a ranar Alhamis
A baya baya nan gwamnonin jihohin yankin arewa maso gabashin Najeriya su ka yi wani taro inda suka jaddada karfafa matakan tsaro domin dakile ayuikan ‘yan bindiga da ke addabar wasu yankunansu.