‘Yansandan kwantar da tarzoma a Kenya sun harba barkonon tsohuwa kan masu zanga-zangar neman Shugaban Kasar William Ruto ya yi murabus a birnin Nairobi, mako guda bayan zanga-zangar kin karin haraji.
Hayakin mai sa hawaye ya turnuke tsakiyar Birnin Nairobi bayan da masu zanga-zangar suka cinna wuta a kan titin Waiyaki, babbar hanyar da ta ratsa tsakiyar babban birnin kasar, tare da jifan ‘yansanda a tsakiyar cibiyar kasuwanci.
A wajen babban birnin kasar, daruruwan masu zanga-zangar sun yi jere cikin yanayi mai zafi a Birnin Mombasa, birni na biyu mafi girma a Kasar Kenya, da ke gabar Tekun Indiya. Sun dauki itatuwan dabino, suna busa kaho na robobi suna buga ganguna suna rera taken “Ruto must go!” wato Dole ne Ruto ya tafi!
Ruto, wanda ke fuskantar rikicin mafi muni a shugabancinsa na kusan shekaru biyu, ya fada ne tsakanin bukatun masu ba da lamuni irin su asusun lamuni na duniya na neman rage gibi, da kuma al’ummar da ke cikin mawuyacin hali na tabarbarewar tsadar rayuwa.