Biyo bayan kadddamar da majasilar dattatawa, inda Sanata Godswill Akpabio da ya fito daga Kudu maso Kudu ya zamo shugaban majalisar, yayin da kuma mataimakinsa Sanata Barau Jibrin, ya fito daga Arewa ta Yamma, an fara gwagwarmar neman sauran mukamai da suka rage a majalisar ta 10.
Sauran manyan mukaman hudu da suka yi saura su ne, kujerar jagoran majalisar da ta mataimakinsa da ta mai tsawatarwa sai kuma ta mataimakin mai tsawatarwa wadanda aka tura su zuwa shiyoyyin Arewa ta Tsakiya, Arewa ta Yamma, Kudu maso Gabas da kuma Arewa maso Gabas
Baya ga Arewa ta Tsakiya da ke a cikin shiyoyin daukacin sauran shiyoyyin tuni sun samu wakilcin sun a manyan mukaman.
Shugaba Bola Tinubu ya fito ne daga shiyayar Kudu maso Gabas, inda kuma da mataimakinsa Kashim Shettima, ya fito daga shiyyar Arewa maso Gabas.
Rabar da manyan mukaman za su lura da na sauran shiyoyyin, sai dai, an bar shiyyar Arewa maso Tsakiya a baya saboda mukamin mataimakin mataimakin shugaban majalisar dattawa da na shugaban majalisar wakilia, sun tafi ne zuwa ga Arewa ta Yamma.
Amma wasu masu fashin baki sun yi jayayya kan cewa, kamata ya yi a ce kamata matsayin Sanata ya kasance jaogoran majalisar dattawa ne zai yi hakan don a yi adalaci, inda wasu kuma suka dage kai da fata cewa, dole ne a bi ka’ida.
A lokacin mulkin marigayi tsohon Shugaban Kasa, Umaru ‘Yar’adua, Aanata Teslim Folarin da ya fito daga Kudu maso Yamma shi ne jagoran majalisar ta dattawa, inda ya ci gaba da rike wannan mukamin har sai da tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan ya cika wa’adin mulkin ‘Yar’adua.
Sanata Bictor Ndoma Egba da ya fito daga Kudu maso Kudu, ya zamo jagoran majalisar bayan an zabi Jonathan a matsayin shugaban kasa.
Bugu da kari, a 2019, Sanata Yahaya Abdullahi daga Jihar Kebbi ta Gabas, shi ne jagoran majalisar kafin ya sauya sheka zuwa PDP, inda kuma Sanata Ibrahim Gobir ya karbi jagorancin.
Ba wani tahrin a siyasar Nijeriya da ya tabbatar da ikirarin na su kan cewa, dole ne sai an mayar da mukamin na jagoran majalisar zuwa shiyyar shugaban kasa.
Har ila yau, idan aka yi dubi da ka’idar zamawo sanata, sanata Abdulfatai Buhari ne ya cancanta ganin cewa ya fito ne daga shiyyar Kudu maso Gabas, duba da ya kasance a majalisar wakilai a 2003, kafin a zabe shi sanata daga 2015 zuwa 2019 da kuma a 2023.
Sanata Solomon Adeola ne ke biye masa a baya, ganin cewa ya taba zama dan majalisar wakilai a 2011 kafin ya zama sanata a 2015, inda kuma aka sake zabarsa a 2015 da 2023.
A shiyyar Kudu maso Gabas kuwa, Sanata Orji Uzor Kalu da Osita Izunaso wadanda suka kasance manyan sanatoci biyu da suka fito daga Kudu maso Gabas, dukkan su sun taba zama a majalisar wakilai da kuma a majalisar datttawa har sau biyu.
Kalu ya taba zama a majalisar wakilai 1993, inda kuma Izunaso ya kasance a majalisar wakilai a 2007.
Lokacin da kawai Kalu ya kasance a majalisar wakilai, ya kai wata uku ne kawai kafin tsohowar mulkin soja ta marigayi Sani Abacha, ta yi juyin mulki.
Hakazalika, sanata Sani Musa da ya fito daga shiyyar Neja ta Gabas da kuma Saheed Umar, da ya fito daga Kwara ta Arewa, sun kasance su ne manyan sanatcin da ke kan gaba.
Daukacin su, sun kasance mayan sanatoci a majalisar dattawa har sau biyu daga 2019 zuwa 2023.
Manyan satocin da suka fito daga shiyyar Arewa ta Gabas, su ne Ahmad Lawan, wanda ya kasance shi ne tsohon shugaban majalisar ta 9 da ta kare sai kuma sanata Ali Ndume.
Sai dai, Lawan ba zai yarda ya zama jagoran majalisar ba, inda a yanzu ya rage ga Ndume, wanda ya ba da gagarumar gudunmawa wajen zamowar Bukola Saraki shugaban majalisar.
Ndume bai yi takara da sanata Danjuma Goje ba wajen neman babban mukamin ba.