Daga Idris Aliyu Daudawa,
Abdulrasheed Maina tsohon shugaban kawo sauyi a al’amuran da suka fansho ya bayyana haka ne ranar Juma’a ma babbar kotun tarayya a Abuja, ya bayyana cewar ‘Ana iya yanke guiwa ta idan ba a bani beli naje na nemi kulawa kamar yadda ya dace.
Maina ya yi wannan bayanin ne ta ahnnun lauyansa Sani Katu, ya bayyanawa mai shari’a Okon Abang lokacin da aka cigaba da sauraren karar jiya a Abuja.
Katu ya bayyanawa kotun cewar an kai shi mutumin da yake karewa asibitin koyarwa na jami’ar Abuja dake Gwagwalada, saboda yadda al’amarin rashin lafiyar sai kara tabarbarewa yake yi, an kuma bayyana halin daya shafi lafiyar sa a takardar neman bada belinsa.
Manema labarai sun bayyana cewar ranar 20 ga watan Janaiiru ne ya nemi mai shari’a Abang, inda ya nemi a bashi wani beli, bayan an kama shi lokacin daya gudu bayan belin da aka ba shi na farko.
Maina a wata takarda wadda aka gabatar ranar 24 ga watan Disamba na shekarar data gabata, wanda lauyansa Anayo Adibe, ya bayyana ita maganar neman beli ta zama dole ne, saboda tabarbarewar al’amarin lafiyar jikinsa.
A takardar tsohon shugaban Hukumar kawo sauyi a harkar fansho ya ce yana da wadanda za su tsaya ma shi, muddin dai aka amince aka ba shi beli wannan ba wani anin damuwa bane.