An zargi wani jami’in hukumar shige da fice ta kasa mai suna Lamba da harbe wani mai zanga-zanga Jacob Bamgbola har lahira a yankin Idigbo da ke Karamar Hukumar Yewa ta Arewa a Jihar Ogun.
PUNCH Metro ta ruwaito cewa Bamgbola yana kan hanyarsa ta kai wata ‘yar kanwarsa a wata unguwa akan babur, sai wasu jami’an shige da fice da ke aiki a shingen bincike a kan babbar hanyar suka tare shi a kan titin Ijowun na babban titin Idiroko inda suka bukaci ya basu Naira 200 kafin su bar shi ya wuce.
- Xi Ya Nanata Bukatar Samun Ci Gaba Mai Inganci A Fannin Tsaron Intanet Da Aikin Sadarwa
- Sin Ta Yi Watsi Da Zargin Da NATO Ta Yi Mata
Wakilinmu ya gano cewa Bamgbola ya ki amincewa da bukatar jami’an, inda ya fada musu cewa ta yaya bai yi wani laifi ba kuma za a karbi kudi har Naira 200 a hannunsa.
Lamarin dai ya haifar da cece-kuce, a can gefe kuma wasu daga cikin jami’an suka ci gaba tambayar sauran masu ababan hawa kudi, sai Benjamin ya yi amfani da wannan damar ya shammace su kawai ya ja babur dinsa zai tafiyarsa.
Lokacin da ya isa wurin da zai je sai a kjiye ‘yar uwar tasa, bayan da Bamgbola ya ajiye ‘yar uwarsa, sai ya ci gaba da ba wa wasu matasan wurin labarin yadda suka yi da da jami’an shige da ficen.
Wata majiya a unguwar ta shaida wa wakilinmu cewa, matasan, wadanda suma sun fuskanci irin wannan matsalar ta karbar kudin da jami’an shige-da-fice suke yi a kan hanyar, sun tara wasu matasa zuwa gidan wani basarake a yankin, Moses Faleye, domin nuna rashin amincewarsu da hakan.
Majiyar ta ce a yayin zanga-zangar, jami’an shige-da-ficen sun kutsa kai cikin harabar, kuma a lokacin da suke kokarin tarwatsa masu zanga-zangar, a wannan yanayi ne aka yi zargin sun harbe Bamgbola har lahira.
Ya ce, “Bamgbola ya je daukar ‘yar ‘yar uwarsa, kuma a kan hanyarsa ta dawowa ya hadu da jami’an shige-da-fice a hanya. Wadannan jami’an koyaushe suna can a shingen binciken. Sun dakatar da shi suna so su karbar masa Naira 200 amma ya ki.
“Ya ce musu shi dan kauyen Otun ne kuma me zai sa ya biya su komai. Bayan ya tafi ne ya kai kara ga wasu matasa inda matasan suka hada kansu zuwa gidan Baale domin yin rajistar kokensu kan ayyukan jami’an.
“Amma cikin ‘yan mintoci kadan jami’an hukumar shige-da-fice sun zo da mota a lokacin da Baale ke kokarin shawo kan lamarin, sai suka fara harbe-harbe, ana cikin haka sai daya daga cikinsu mai suna Lamba ya harbe Bamgbola. Matasan sun garzaya da Bamgbola asibiti inda a wannan lokacin lilkitoci suka tabbatar da ya rasu.”
Shugaban kungiyar ‘yan banga a garin, Adesina Alabi, yayin da ya koka kan faruwar lamarin, ya ce jami’an tsaro na sha’awar karbar kudade daga masu amfani da hanyar a kan hanyar.
“Kawai za ka ga ’yan sanda, jami’an Kwastam, jami’an shige-da-fice, da sauran su kawai babu abin da suke yi sai katbar kudi a shingayen hanya daga hannun masu ababen hawa. Yana kara yawa,” inji shi.
Da aka tuntubi Falaye, ya ce lamarin da ya yi sanadiyyar mutuwar Bamgbola abin takaici ne, inda ya ce kamata ya yi a sasanta lamarin.
Ya ce, “A gaban gidana lamarin ya faru. Matasan garin sun zo ne domin nuna rashin jin dadinsu kan ayyukan jami’an shige da fice a yankinmu.
“A lokacin da nake kokarin sasanta su, wasu jami’an shige-da-fice sun zo, da suka ga matasan sai suka fara harbin iska. Ana cikin haka ne harsashin ya samu mutum daya ya mutu.
“Bayan faruwar lamarin, an kai rahoton lamarin a ofishin ‘yansanda na Igbokofi kuma ‘yan sandan sun zo da kyamarori kuma sun karbi bayanai daga gare mu.”
Jami’ar hulda da jama’a ta rundunar ‘yan sandan jihar, SP Omolola Odutola, ta shaida wa wakilinmu cewa ba ta da masaniya a kan lamarin, amma ta yi alkawarin za ta nemi wakilinmu da zarar lamarin ya zo gare ta.
Har ya zuwa lokacin kammala wannan rahoton ba ta ce komai ba.
Da aka tuntubi mai magana da yawun NIS a Jihar, Olajide Oshifeso, ya ce, “an riga an fara bincike kan lamarin kuma idan an kamala za a bayyana wa jama’a cikakkun bayanai.”