Mai koyar da ‘yan wasan kungiyar kwallon kafa ta Real Madrid Carlo Ancelotti ya amince da karbar ragamar horar da tawagar ‘yan wasan kasar Brazil a shekara ta 2024, in ji shugaban hukumar kwallon kafa ta kasar, Ednaldo Rodrigues.
Brazil, wadda ta lashe gasar cin kofin duniya sau biyar ta yi amannar cewa dan kasar Italiyan shi ne ya fi dacewa da ya kai Brazil Copa America da za a yi a watan Yunin 2024.
- Kiwon Lafiya: Yadda Dabi’un Ko-in-kula Ke Yi Wa ‘Yan Nijeriya Kisan Mummuke
- Ribadu Zai Shugabanci Taron LEADERSHIP Da NDLEA Kan Yaki Da Miyagun Kwayoyi
Rodrigues ya ce mai koyarwa Fernando Diniz zai ci gaba da lura da kungiyar ta Brazil da ake kira Selacao tare da ci gaba da aikinsa na horar da Flumine har zuwa lokacin da Ancelotti zai karbi aiki wato idan kwantiraginsa ya kare da Real Madrid.
“Shi ne zai mika wa Ancelotti ragamar Brazil kuma salon wasansa ya yi kusa da na kocin da zai karbi aikin kai kungiyar gasar cin kofin Copa America, wato mista Ancelotti” in ji Rodrigues.
Ya ci gaba da cewa ba za su kira shi kocin rikon kwarya ba ga tawagarsu ta kasa,
Brazil dai ta kasance ba ta da mai koyarwa tun bayan kammala gasar kofin duniya da aka kammala a bara, lokacin da Tite ya ajiye aiki bayan cire kasar da Croatia ta yi a wasan kusa da daf da na karshe.
Kocin da ke jan ragamar tawagar ‘yan kasa da shekara 20 ne ke lura da Brazil a wasanni sa da zumunta da take yi a kwanakin nan kuma Ancelotti mai shekara 64 ya koma Real Madrid ne a shekarar 2021 bayan ya bar Eberton, kuma tun bayan komarwarsa ya ci Champions da La Liga da Copa del Rey da sauransu.
Da kofin zakarun Turai da ya lashe a 2022 a wasan karshe a hannun Liberpool, Ancelotti ya lashe kofin nahiyar Turai na hudu kenan a matsayinsa na koci, na biyu a Real Madrid bayan biyu da ya lashe a AC Milan.