Mataimakin kakakin Majalisar wakilai ta tarayyar Nijeriya a zauren Majalisa karo na tara, Honarabul Ahmed Idris Wase ya yi ikirarin cewa Jam’iyyarsu ta APC za ta yi nasara da rinjaye mai girma a zaben shugabancin majalisar ta 10 da za a rantsar.
Dan Majalisar mai wakiltar mazabar Wase ta Jihar Filato, kuma wanda ya kasance daya daga cikin yan takarar Kujerar shugabancin Majalisar wakilai a zauren Majalisar, ya bayyana hakan ne a wani zantawar sa da manema labarai a garin Abuja.
Idris Wase, ya kara da cewa a bisa shirye-shiryen da su ke, sun samu gabatar da taro na niyyar su ta neman shugabancin Majalisar Kasa na kujerar kakakin Majalisar wakilan tarayyar kasar kuma suna ganin sun kai gabar da ya kamata su fada wa mutane ‘yan Jam’iyyar su, masoya tare da magoya baya cewa lokaci ya kai.
“Duk da cewa akwai ‘yan Jam’iyyar adawa da su ma suke ganin za su iya hada kai su nema, ina mai tabbatar da cewa Jam’iyyar APC ce za ta yi nasara da rinjaye ta samu shugabancin Majalisar.”
“A game da Batun Shiyya-Shiyya wacce uwar Jam’iyya ta ke kokarin shirin yi, mun san wani abu ne wanda ya saba wa ka’idar kundin tsarin mulkin Nijeriya domin sashe na 14 cikin 3, ya bayyana cewa ya kamata a raba mukamai bisa ga shiyyoyi ko Jihohi idan zai kai amma idan ba zai kai ba shi ne za a yi bisa ga shiyya-shiyya.
“Don haka wannan shi ne tsarin da muke da shi na Jagorancin shugabancin Kasa na shugaban kasa, shugaban Majalisar Dattijai da Majalisar wakilai Hakazalika da na mataimakan su wanda su ne guda shida domin kawo tsarin zaman lafiya da ingancin zamantakewa amma kamar an manta da wannan Dokar.”
“Ni dan Jam’iyya ne kuma na yarda da tsarin dokokin Jam’iyya kuma na tabbata idan Jam’iyya ta yi za mu yi kuma dama can yan Majalisa ne ke da hakkin yin zaÉ“e kamar yadda kundin tsarin mulkin ya tanada kuma duk abin da ake yi ana tuntuba ne domin a ga yaya za a yi a kai ga nasara ta yadda ba za a samu hayaniya ba domin zaÉ“e ba ya gabata sai an Shiga cikin Majalisa.” In ji Shi.
Acewar Idris Wase, kamar yadda ya zo ya bayyana cewa yana neman shugabancin Majalisar, ai akwai wadanda su ma suka zo suna nema daga Jam’iyyarsu ta APC wanda suke da kyakkyawar alaka da tunani don haka ya kamata su hada kai su fitar da wanda suke ganin zai iya yin aikin daga cikin su shi yasa suke tattaunawa a kai.