Jam’iyyar APC a Jihar Kogi, ta amince da dakatar da wani jami’in jam’iyyar na kasa, Murtala Yakubu da ‘yan majalisar zartarwa na mazabarsa ta Ajaka ta 1 a Karamar Hukumar Igalamela/Odolu.
Yakubu wanda shi ne Mataimakin Sakataren Yada Labarai na Jam’iyyar APC na kasa, shugabannin gundumar Ajaka ta 1 sun dakatar da shi ne ta hanyar wata wasika mai dauke da kwanan watan Maris 20, 2023 bisa zargin cin zarafi, rashin biyayya, rashin da’a da rashin bin tsarin jam’iyya.
- Kotu Ta Karbi Kararrakin Zabe 6 A Kebbi
- CBN Ya Saki Kudi, Ya Umarci Bankunan Kasuwanci Su Yi Aiki A Ranakun Mako
Da yake tabbatar da matakin da shugabannin jam’iyyar a mazabar Ajaka suka dauka, shugabannin jam’iyyar APC na jihar a wata sanarwa da Sakataren Jihar, Hon. Joshua Emmanuel, ya ce saboda haka, an hana Yakubu shiga dukkan harkokin jam’iyyar.
Sanarwar mai taken “Amincewa da kuma tasirin dakatarwar da jam’iyyar APC ta yi wa Hon. Muritala Yakubu (Ajaka) a wani bangare na cewa, “Kwamitin zartaswa na jam’iyyar APC reshen Jihar Kogi ya takardar Dakatar da Hon. Muritala Yakubu (Ajaka) daga kwamitin zartarwa na karamar hukumar IGALAMELA/ODOLU.
“Kwamitin zartaswa na jam’iyyar APC reshen jihar Kogi, bayan da ya yi la’akari da gaskiyar lamarin da ake zargi ya kuma tabbatar da gaskiyarsa da kuma girman ayyukan da aka yi masa na adawa a jam’iyyar, ya amince da matakin ladabtarwa, wato dakatarwar da jam’iyyar ta yi masa.
“Ana sa ran hukuncin da aka zartar masa zai zama darasi ga wasu.”