Shugaban riƙon ƙwarya na PDP, Amb. Umar Iliya Damagum, ya zargi jam’iyyar APC da cewa rikicin cikin gida ya hana ta gudanar da taron koli (NEC) tsawon shekaru biyu. Ya bayyana hakan yayin karɓar sabbin mambobi daga APC da NNPP a Nguru, Jihar Yobe, yana nuna rashin amincewa da iƙirarin rikici a cikin PDP.
Damagum ya yi watsi da rahotannin rikici a PDP, yana mai cewa labarun “ƙanzon Kurege” ne kuma jam’iyyarsa akwai haɗin kai. Ya ƙara da cewa PDP ta kasance jam’iyya mafi ƙarfi fiye da sauran jam’iyyu, inda ta shiri don tunkarar zaɓen 2027.
- Rikicin PDP: Kotu Ta shiga Tsakani, Ta Hana Tsige Damagun
- Yadda Gwamnonin PDP Suka Ceto Damagun Daga Kora
A wani ɓangaren, shugaban ya zargi APC da yaudarar al’ummar Nijeriya, yana mai cewa mulkin ta ya haifar da matsin tattalin arziƙi matsalar tsaro. Ya ƙara da cewa PDP ita ce mafificiyar jam’iyyar siyasa da ƴan Nijeriya ke so, inda ta ke da damar biyan buƙatun al’umma.
A karshe, Damagum ya yi kira ga dukkan ‘yan siyasar da suka tafi zuwa wasu jam’iyyu da su dawo gida, yana mai cewa PDP ita ce kaɗai jam’iyyar da za ta iya taimakawa wajen magance matsalolin Nijeriya. Ya tabbatar da cewa jam’iyyar tana shirye don tunkarar zaɓen 2027.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp