Jam’iyyar APC ta musanta jita-jitar cewa Shugaba Bola Tinubu na shirin sauya mataimakinsa, Kashim Shettima, a zaɓen 2027. Alhaji Bala Ibrahim, Daraktan Watsa Labarai na APC, ya bayyana hakan a wata hira da jaridar Daily Trust, inda ya ce wannan batu raɗe-raɗi ne kawai wanda ba shi da tushe.
Ya ƙara da cewa maganganun da ake yi game da wannan batu na “teburin mai shayi” ne, wanda bai kamata a ɗauki su da gaske ba.
Alhaji Bala Ibrahim ya tabbatar da cewa idan Shugaba Tinubu zai yanke shawarar sauya mataimaki, wannan ba zai kasance yanke shawara guda ɗaya ba, sai an tattauna da dukkan masu ruwa da tsaki.
A hasashen idan za’a sauya mataimakin za’a ɗauki mai farin jinin da zai iya kawo wa shugaba Tinubu ƙuria a zaɓen 2027.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp