Tsohon dan wasan kungiyar kwallon kafa ta Arsenal Paul Merson, ya bayyana cewa kungiyar wadda mai koyarwa Mikel Arteta yake koyarwa ba zata iya tabuka komai ba a kakar wasan bana duba da irin yadda ake doke ta a wasannin da basu kamata tayi rashin nasara ba.
Manchester City ta doke Arsenal da ci 1-0 kuma wannan shine wasa na 18 a jere a dukkan wasannin da ta fafata, bayan da ta ci Arsenal din bayan Arsenal ta karbi bakuncin Manchester City a wasan mako na 25 a gasar Premier League da suka fafata a filin wasa na Emirates.
Minti biyu da fara wasa Manchester City ta zura kwallo a ragar Arsenal ta hannun dan wasan Ingila Raheem Sterling, wanda ya dade yana cin Arsenal idan suka hadu a wasa kuma a haka aka tashi babu kungiyar da ta sake zura kwallo a raga.
Manchester City ta yi nasara a wasanni 11 da ta buga a waje ba tare da an doke ta ba a karon farko tun bayan bajintar da ta yi tsakanin watan Mayu zuwa Nuwambar shekara ta 2017 duka a karkashin mai koyarwa Pep Guardiola.
Tun bayan da kungiyar ta Etihad ta tashi 1-1 da West Brom a gasar Premier cikin watan Disambar shekarar 2020 data gabata, tun daga lokacin Manchester City ta lashe karawa 18 a jere a dukkan fafatawa.
Manchester City ta ci gaba da zama ta daya a kan teburi da tazarar maki 10, bayan saura fafatawa 13 a karkare kakar wasa ta bana ita kuwa Arsenal tana nan matakinta na 10 da tazarar maki shida tsakaninta da ‘yan shidan farko a gasar bana.
Sai dai tsohon dan wasan kungiyar, Paul Merson, ya bayyana cewa kungiyar ta Arsenal ba zata iya buga abin arziki ba a kakar wasa ta bana duba da irin rashin nasarar da kungiyar ta keyi kuma hakan yasa yake ganin abune mai wahala kungiyar ta iya samun tikitin kofin zakarun turai na kakar wasa mai zuwa.
“Abu ne mai wahala Arsenal karkashin Arteta sun iya kai kungiyar ga nasara idan har a haka zasu ci gaba da tafiya suna rashin nasara a wasannin da basu kamata ba kuma babu tabbas idan zasu iya samun tikitin zakarun turai na kakar wasa mai zuwa” in ji Merson
Ya kara da cewa “Kowa yayi zaton Arsenal zata shiga sahun manyan kungiyoyin da za’a fafata dasu wajen neman lashe gasar firimiyar Ingila idan aka kalli yadda suka hada matsan ‘yan wasa da kuma salon yadda suke buga wasa.”
Sai dai kociyan kungiyar Mikel Arteta yana da kwarin gwiwa inda bayan tashi daga wasan ya bayyana cewa duk da haka yana ganin za suyi abin kirki a kakar wasan ta bana kafin a kammala bugawa.