Abba Ibrahim Wada" />

Arsenal Ta Na Zawarcin Antonio Valencia

Rahotanni daga kasar Ingila sun bayyana cewa kungiyar kwallon kafa ta Arsenal tafara zawarcin dan wasan baya na kungiyar kwallon kafa ta Manchester United wanda kwantaraginsa zai kare a karshen wannan kakar.
Kwantaragin Balencia zai kare a kungiyar a karshen kakar wasa wanda hakan yake nufin zai kawo karshen zaman shekara goma da yayi yana zaman kungiyar wadda yayiwa wasanni sama da 300 a gaba daya wasannin daya buga mata.
Balencia ya lashe gasar firimiya guda biyu sai gasar cin kofin kalubale na FA da kuma gasar cin kofin Europa sannan kuma ya lashe kyaututtuka da dama a zamansa a Manchester United tun a shekara ta 2009
Kamar yadda rahotanni suka bayyana Arsenal tana daya daga cikin kungiyoyin da suke zawarcin Balencia wanda a shekarun baya ya kware wajen buga bangaren dama a baya duk da cewa da farko dan wasan gaba ne.
A kwanakin baya mahaifin dan wasan ya bayyana cewa kungiyoyin Westham da Inter Milan da kuma wata kungiya daga kasar Sin wato China suna zawarcin dan wasan wanda yakoma Manchester United daga Wigan.
Bayan Ronaldo yabar United ne a shekara ta 2009 Manchester United ta siyo Balencia domin ya maye gurbinsa bayan yakoma Real Madrid sai dai burin na United akansa bai samu ba inda ya koma dan wasan baya tun lokacin tsohon kociyan kungiyar Sir Aled Ferguson.

Exit mobile version