Wasu sun san garuruwan da ake kira ‘Hausa Bakwai’ da ‘Banza Bakwai’ amma ba su san dalilin da ya sa ake kiransu da wadannan sunayen ba.
Wannan ne ya sa naga dacewar yin wannan dan takaitaccen bayanin kamar yadda na taba karantawa a littafin ‘Kano Ta Dabo Cigari’ na Marigayi Wazirin Kano Alhaji Abubakar.
- Ya Kashe Limami Saboda Ya Hana Su Shan Wiwi A Kusa Da Masallaci A Kano
- Zargin Sata: Jami’an ‘Yansanda A Kaduna Sun Kama Buhunan Taki Guda 600
Bayan Bayajidda ya gudo daga Kasar Borno shi da matarsa mai suna Magaram saboda yunkurin kashe shi da Sarkin (Shehu) Borno ya yi, sai suka zo wani gari da ake kira Garun Gabas a ƙasar Hadeja. A nan ya bar matarsa saboda tsohon cikin da take dauke da shi ya wuce Daura. Bayan ya isa Daura cikin dare, ya sauka a gidan wata tsohuwa, sai ya nemi ruwa amma bai samu ba. Tsohuwar take faɗa masa dalilin da ya sa basa samun ruwa sai sau daya a sati saboda wata macijiya da take hana ɗibar ruwan. Da Bayajidda yaji haka, sai ya karɓi guga a wajen tsohuwar, ya nufi rijiyar Kusugu inda macijiyar take ciki, ya kashe ta ya ɗebi ruwa. Da gari ya waye, Sarauniya Kabara (wacce take mulkin Daura) ta ji labari, sai ta sa aka yi bincike aka gano Bayajidda ne ya kashe macijiyar. Ta kirasa ta ce za ta basa rabin mulkinta. Amma ya ƙi amincewa, ya ce mata sai dai a daura musu aure da ita idan ta amince. Sarauniya ta yarda, aka daura musu aure da Bayajidda. Sai jama’ar garin suka fara kiransa da ‘Makas-Sarki.’ Daga baya kuma suka koma ce masa ‘Sarki’ kawai. To daga nan ne aka samo kalmar Sarki da ake fadawa wasu sarakuna a yau. Da Sarauniya Kabara ta haifi da namiji, sai aka sanyawa yaron suna Bawo.
A lokacin da Bawo yake mulkin Daura, an yi wata masifaffiyar yunwa a Kasar Hausa, wacce ta zama babu inda ake samun abincin mai yalwa sai a wani wuri wanda shi ne Kano a yanzu. Don haka kabilu suka riƙa ƙaura zuwa wurare masu ɗan yalwan abinci domin su tsira da rayuwarsu. Bayan jama’a sun fita kowa ya samu in da ya fake, sai ya zamana babu shugabanci kowa zaman kansa yake. Daga nan sai zalunci ya yawaita a tsakanin jama’a. Masu karfi su kwace kayan raunana. Wannan ne ya sa raunana suka fara kai kukansu Daura wajen Sarkin Bawo.
Da kararraki suka yawaita, sai Sarki Bawo ya yi shawarar kafa shuwagabanci a dukan wadannan wuraren da abin ya dama. Sai ya tura dansa Bagauda zuwa Kano, ya tura dansa Gunguma zuwa Zariya, ya tura ɗansa Duma zuwa Gobir, ya tura ɗansa Kumayo zuwa Katsina, ya bawa ɗansa Gazori riƙon Daura, ya bawa dansa Zamna Biram, ya tura dansa Kogo zuwa Rano. Wadannan garuruwa da Sarki Bawa ya bawa ‘ya’yansa ko ya tura su, su ake kiran Hausa Bakwai.
Akwai kuma Banza Bakwai, wanda Sarki Bawo ya sake tura wasu ‘ya’yan nasa bakwai zuwa can. Sai dai kuma wasu masana sun ce ba ‘ya’yansa na cikinsa ba ne, ‘ya’yan dan uwansa mai suna Karaf-da-gari ne wanda Bayajidda ya haifa da wata baiwarsa mai suna Bagwariya. Wadannan garuruwa bakwai da aka tura ‘ya’yan su ne: Zamfara da Gwari da Nupe da Yaruba (ilori) da Kwarrafa da Kebbi da Yawuri. Su ne ake kira Banza Bakwai.
Wannan shi ne asalin yadda aka samo sunan ‘Hausa Bakwai’ da kuma ‘Banza Bakwai’.
Mohammed Bala Garba, Maiduguri
Dalibi daga Jami’ar Tarayya ta Maiduguri (UNIMAID). 08098331260.