Daliban jami’o’in Nijeriya an tilasta masu rasa karatu har na tsawon shekara hudu wannan sakamakon yawan yajin aikin da Kungiyar Malaman jami’o’i ta Kasa (ASUU), suke tafiya tun lokacin da aka dawo mulkin farar hula gadan- gadan a shekarar 1999.
Binciken da Jaridar LEADERSHIP ta yi ya nuna yajin aikin da kungiyar ASUU take yi a halin yanzu shi ne na goma 16 tun da Nijeriya ta koma mulkin dimokuradiyya a shekarar 1999.
An rufe jami’o’in gwamnati fiye da shekaru 4 cikin shekara 23, wanda lokaci ne da ya kamata a ce an kammala karatun digiri, yayin da ake samun yajin aikin da yake kai makonni, wani yajin aikin kuma yake kai watanni.
Yawan yajin aiki mai dadewa da kungiyar ASUU take yi abu ne wanda yake damun dalibai, iyayensu, da kuma masu ruwa da tsaki kan al’amarin da ya shafi ilmi.
Shekaru da yawa jami’o’in Nijeriya sun sha fuskantar matsaloli na rashin ba su kudaden da suka kamata a ba su don gudanar da ayyukansu. Ga dai kuma rashin isassun kayan da suka dace a ce suna amfani da su, wannan kuma abin an dade ana fuskantar hakan tun daga gwamnatocin da suka shude, abin har yanzu an rasa yadda za a maganin al’amarin.
ASUU kungiya ce ta ma’aikata wadda aka kafa ta shekarar 1978 domin ta kare muradan malaman jami’o’in gwamnatin tarayya da na Jihohi, saboda kuwa babbar manufarsu ita ce kare mutuncinsu da kuma mu’amala tsakanin malaman jami’o’i da wadanda suka daukesu aiki, al’amarin da kullum yana kasancewa zaman doya da manja.
A karskashin mulkin Shugaban Kasa Muhammadu Buhari, dalibai da ke karatu a jami’o’in Nijeriya sun rasa zagon karatu na watanni 13.
Hakan ya faru ne sanadiyar yajin aikin da Kungiyar ASUU ke tsunduma. Shi ya sa kwararru a bangaren ilimi suke cewa wadanda suka kammala karatunsu a jami’o’in Nijeriya, ba a daukarsu da wata daraja kamar wadanda suka yi karatu a kasashen waje.
Karkashin mulkin Shugaban Kasa Buhari, kungiyar ta fara shiga yajin aiki ne a ranar 17 ga Agustan 2017, bayan da gwamnati ta ki cika masu alkawarin da suka sa hannu a yarjejeniyar da suka yi.
Daga cikin fiye da naira tiriliyan daya da ASUU ta bukaci a ba ta, naira biliyan 200 ne kadai aka ba ta wannan kuma shi ne ya sa kungiyar ta shiga yajin aikin gargadi a watan Nuwamba 2016, domin a biya masu bukatunsu. An koma aiki ne a watan Satumba 2017.
Yajin aikin kungiyar ASUU na biyu an fara shi ne ranar 4 ga Nuwamban 2018, wanda ya kai zuwa 7 ga Fabarairun 2019, an yi kwana 95, wannan kuma ya faru ne sakamakon wasu al’amuran da ba a gama da su ba tsakanin gwamnatin tarayya da kungiyar na yarjejeniya da aka sa hannu ga bangarorin biyu a shekarar 2013.
A yanzu haka dai, sanadiyar yajin aikin ASUU, Kungiyar Kwadago ta Kasa (NLC) za ta fara zanga- zangar goyon bayan a ranar 26 ga watan Yulin 2022.
Kungiyar ta ce babbar matsalar ita ce, rashin cika alkawarin da gwamnatin tarayya ta sa hannu da maganar aiwatar da su a shekarar 2019, domin kuwa dukkan jami’an gwamnati da na kungiyar sun amince da hakan.
Wadannan kuma sun hada da wani tsarin biyan su albashi da alawus da jin dadinsu da samun ‘yancin kan da ya shafi harkokin koyarwa da dai sauran su.
Bugu da kari binciken LEADERSHIP ya gano cewa saboda yawan tafiya yajin aiki da kungiyar take yi, yanzu wasu dalibai sun gwammace shiga aikata laifuka, yayin da wasu kuma suka zama kamar wadanda ba su taba yin karatu ba. Duk da haka akwai wadanda har yanzu ba su fid da ran abubuwan da suka shafi ilimi na iya gyaruwa a Nijeriya.
Bugu da kari, binciken LEADERSHIP ya nuna cewa an fara yajin aikin ASUU na farko a shekarar 1988, lokacin da ta yi zanga- zanga dangane da mulkin Janar Ibrahim Badamasi Babangida wajen samun albashin da ya dace da kuma ba ta ‘yancin da ya dace. Hakan shi ya sa aka soke kungiyar ASUU a ranar 7 ga Agustan 1988 tare da kwace duk wasu kaddarorinta.
An ba ta damar sake ci gaba da harkokinta a 1990, sai dai bayan wani yajin aikin an sake soke kungiyar a ranar 23 ga Agustan 1992.
Amma bayan wata yarjejeniyar da aka cimma a ranar 3 ga Satumban 1992 wanda aka biya hakkokin kungiyar masu yawa da suka hada da damar da ma’aikata suke da ita na zauna da su wajen tattauna bukatunsu.
Duk korafi da maganganun da kungiyar ASUU suke yi dangane da yajin aiki, abin ya fi maida hankali ne kan kudaden da ake ba su da kuma gyara a jami’oin gwamnati har ma da wasu alawus da ta ce ariyas na kudaden sun kai naira biliyan 92 a wancan lokacin.
A halin ake ciki yanzu kudaden sun wuce haka, saboda kudaden ariyas din da suke bi ba a biya su ba tun daga shekarar 2016.