Bello Hamza" />

Asirin Farfesan Da Ya Nemi Yin Lalata Da Dalibarsa Ya Tonu

Wani malami a jami’ar Obafemi Awolowo Unibersity (OAU) ta garin Ile-Ife dake jihar Osun Farfesa Richard Akindele, ya fada takaddamar badalar jima’i, bayan da aka zarge shi da neman ya yi jima’i da wata dalibarsa kafin ya bata makin da zai kai ta ga cin jarawar daya shirya wa ajinsu.

Bayanin da aka samu na tattaunawar da suka yi tsakaninsu a wani faifai da yake yawo a tsakin jama’a, an ji Farfesan yana cewar sai ya yi jima’i sau 5 da ita in har tana son ta ci jarabawar in ba haka ba kuma zata fadi jarabawar kai tsaye, amma dalibar nan take ta ki yarda da bukatar malamin, tana mai cewa, wannan bukata ya yi mata tsauri.

Duk kokarin ganin dalibar bai yi nasara ba sanan kuma Farfesan ya yi gum da bakinsa ya ki fadin komai, sai dai wadanda suka san muryar Farfesar sun ce lallai muryar da ke magana a faifan ta Farfesa Akindele.

Hukumar jami’ar ta bayyana fara binciken wannan badalar, ta ce duk wanda aka samu da hannu a cikin badalar za a hukunta shi yadda ya kamata.

Jami’in hulda da jama’a na jami’ar, Mista Abiodun Olanrewaju ya bayyana wa majiyar tamu cewa, jami’ar na sane da faifai da ke yawo a cikin al’umma kuma tuni a ka shiga binciken lamarin domin hukunta wanda yake da hannu.

Ya ce, “jami’ar OAU ba ta lamunce da badala da dalibai ba, muna sane da faifain da ke yawo in da wani mutum da wata mace ke magana har macen ta ambaci wani suna”

“Muna bin diddigin wannan faifai domin gano sahihancinsa, da zaran mun tabbatar da sahihancinsa, hukumar jami’ar ba zata yi wata-wata ba wajen hukunta duk mai hannu a cikin wannan abin kunyar”

Exit mobile version