ASNIM Ta Shirya Taron Wayar Da Kai Kan Hikimar Yin Da’awa

A karshen makon da ya gabata ne kungiyar ‘Yan’uwa Musulmi Ta Kasa da a ka fi sani da “Association of Nigerian Muslims” a Turance ko kuma ASNIM a takaice, ta kammala wani taron wayar da kai na yini biyu da ta shirya ta gudanar zauren taro na “Youth Center” a cikin garin Keffi, Jihar Nasara, inda a ka tattaunawa a kan batutuwan da su ka shafi harkar Da’awa da su kansu masu Da’awar.

Taken taron shi ne “Matsayin Malaman Musulunci A Fagen Da’awa”. Yayin taron wanda ya gudana tsakanin Asabar da Lahadin da suka gabata, , an bai wa malamai daban-daban damar gabatar da mukalu don amfanin jama’a musamman ma mahalarta taron.

Malam Muhammad bn Umar (Abu Rahma) shi ne jagoran wannan kungiya reshen Jihar Nasarawa kuma mai masaukin baki, ya yi wa wakilinmu karin bayani game da  dalilin shirya wannan taro da kuma muhimmancinsa, inda ya ce, an shirya taron ne don zaburar da matasa game da sha’anin da’awa, tare da cewa irin wannan taro na wanzar da sanayyar juna da kuma karfafa zumunta a tsakanin al’ummar Musulmi kasancewa ya na hado kan jama’a daga sassa daban-daban.

Daga nan, Malam Muhammad ya jaddada buktar da ke akwai al’umma su rika mara wa irin wannan taro baya a duk lokacin da ya taso don a gudu tare a tsira tare.

Yayin rufe taron, an mika satifiket ga wandanda suka samu yin rijistar shiga taron kyauta.

Bakidaya manyan malaman da suka halarci rufe taron sun yi kira ga jama’ar Musulmi da a kasance masu hadin kai da son juna a kowane lokaci. Taron ya samu mahalarta daga ciki da wajen garin Keffi, sannan ya gudana cikin salama.

Exit mobile version