Wasu manyan ƴan siyasa daga jam’iyyun adawa sun hallara a Cibiyar Yar’Adua da ke Abuja a yau Laraba da rana don taron ƙaddamar da sabbin shugabannin jam’iyyar African Democratic Congress (ADC), a wani mataki na shiryawa zaɓen shekarar 2027. Taron ya samu halartar manyan fitattun ’yan takara da tsofaffin gwamnoni daga sassa daban-daban na ƙasa.
Cikin waɗanda suka halarta akwai Atiku Abubakar na jam’iyyar PDP; Peter Obi na LP; tsohon gwamnan Jihar Kaduna, Nasir El-Rufai; da tsohon Ministan Sufuri kuma gwamnan Rivers, Rotimi Amaechi. Haka kuma, Solomon Dalung, Dino Melaye, Dele Momodu, Sanata Gabriel Suswam, da Sanata Ireti Kingibe sun samu halarta. Emeka Ihedioha da Air Marshal Sadique Abubakar (rtd.) suma sun bayyana.
- David Mark Da Aregbesola Sun Zama Shugaba Da Sakataren Jam’iyyar ADC
- Ana Sa Ran Samun Bunkasuwar Dangantakar Sin Da Kungiyar SADC
A yayin taron, an sanar da cewa haɗakar jam’iyyun adawa ta ɗauki jam’iyyar ADC a hukumance a matsayin dandalin siyasa da za ta yi amfani da shi don ƙalubalantar jam’iyyar APC a 2027. An bayyana tsohon Shugaban Majalisar Dattawa, David Mark, a matsayin shugaban riko na ƙasa. Ya fice daga jam’iyyar PDP domin jagorantar sabon tsarin siyasar.
An kuma nada tsohon gwamnan Osun kuma jigon APC, Rauf Aregbesola, a matsayin sakataren riko na ƙasa, alamar yiwuwar sauyin tunani da haɗewar ƙarfi daga jam’iyyu daban-daban. Ana sa ran David Mark da sauran shugabanni za su fara ƙaddamar da sabuwar tafiyar siyasar, yayin da taron ke ci gaba a lokacin haɗa wannan rahoto.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp