• English
  • Business News
Sunday, September 14, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Atiku: ‘Yan Nijeriya, Tsakanin Mulkin PDP Da APC, Wanne Ya Fi Bala’i?

by Sulaiman
3 years ago
in Siyasa
0
Atiku: ‘Yan Nijeriya, Tsakanin Mulkin PDP Da APC, Wanne Ya Fi Bala’i?
Share on FacebookShare on TwitterShare on WhatsAppTelegram

Ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar PDP, Atiku Abubakar, ya yi kira ga jama’ar Jihar Neja da sauran ‘yan Nijeriya da su tuno da shekaru 16 na mulkin PDP kuma su kwatanta su da shekaru bakwai na mulkin gwamnatin APC da ya kawo matsananciyar damuwa da talauci da rashin tsaro acikin al’ummar Nijeriya. 

Daga nan ya yi kira ga ‘ya’yan jihar da ma ‘yan Nijeriya baki ɗaya da su tabbatar sun aje kyakkyawan tarihi da kyautata wa ‘yan baya ta hanyar korar gwamnatin APC ta hanyar ƙin zaɓen dukkan ‘yan takarar ta a zaɓuɓɓukan da za a yi a watan gobe.

  • 2023: Atiku Ya Sha Alwashin Ƙara Wa Jihohi Da Ƙananan Hukumomi Ƙarfin Iko

Atiku ya yi wannan kalamin ne a wajen taron yaƙin neman zaɓen PDP da aka yi a Minna, babban birnin Jihar Neja, a ranar Asabar.

Labarai Masu Nasaba

PDP Ta Dage Kan Gudanar Da Taronta Duk Da Sabbin Sharuɗɗan Da Ɓangaren Wike Ya Gindaya

INEC Ta Amince Da David Mark A Matsayin Shugaban ADC

Akwai alamun cewa filin Kasuwar Bajekoli da ke unguwar Shango a garin Minna bai taɓa ganin dandazon mutane ba irin wanda ya gani a ranar Asabar wajen karɓar baƙuncin Atiku da Gwamna Arthur Ifeanyi Okowa na Jihar Delta.

Rundunar yaƙin neman zaɓen Atiku/Okowa ta isa Minna ne a ranar Asabar inda jama’a su ka yi dafifi domin tarbar su ta yadda filin ya cika ba masaka tsinke.

Tun misalin ƙarfe 8 na safe magoya bayan jam’iyyar su ka cika filin Kasuwar Bajekolin, a yayin da wasu kuma su ka nufi babban filin jirgin sama na Minna mai nisan kimanin kilomita daga cikin gari domin tarbar Atiku da Okowa, da kuma sauran manyan baƙi da su ka haɗa da tsohon Shugaban Majalisar Dattawa, Abubakar Bukola Saraki, Gwamna Aminu Waziri Tambuwal na Jihar Sokoto, Gwamnan Jihar Akwa Ibom, Emmanuel Udom, da tsofaffin gwamnoni Boni Haruna na Adamawa, Liyel Imoke na Kuros Riba, Malam Ibrahim Shekarau na Kano, da sauran su da dama.

Filin Kasuwar Bajekolin da ke Shango ya cika maƙil da dubban magoya bayan jam’iyyar PDP. Wasu ma daga wajen filin su ka tsaya, wanda hakan ya jawo cinkoson motoci cika a kan manyan hanyoyin Minna.

Tsohon gwamnan Neja, Dakta Mu’azu Babangida Aliyu (Talban Minna), wanda shi ne shugaban rundunar yaƙin neman zaɓen PDP a jihar a zaɓen 2023, shi ma ya yi kira ga jama’a da su fitar da APC daga mulkin jihar domin, a cewar sa, ba ta tsinana komai ba sai jawo baƙin ciki da wahala ga jama’a.

Sauran waɗanda su ka yi jawabi a taron sun haɗa da mataimakin Atiku a takara, wato Gwamna Okowa, da Shugaban PDP na ƙasa, Dakta Iyorchia Ayu, da Gwamna Aminu Tambuwal, da Dino Melaye, da Gimbiya Rakiya Atiku (maiɗakin Atiku Abubakar) da Sanata Zaynab Kure, da shugaban PDP na Neja, Tanko Beji, da Gwamna Emmanuel Udom na Akwa Ibom, da sauran su, waɗanda kowannen su ya shawarci masu zaɓe a jihar da su fitar da APC daga mulkin jihar da ma tarayya.

An ƙawata taron da hawan raƙuma da dawakai da raye-rayen gargajiya da waƙoƙin mawaƙa irin su Naziru Sarkin Waƙa da sauran su.

A ƙarshe, Dakta Babangida Aliyu ya shirya wa Atiku da sauran jiga-jigan jam’iyya walimar cin abincin rana a gidan sa.

Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

Shiga zaurenmu na WhatsApp

ShareTweetSendShare
Previous Post

Yanzu-yanzu: PDP Ta Bukaci Gaggauta Cafke Tinubu Kan Zargin Safarar Miyagun Kwayoyi

Next Post

Wa’adin Canjin Kudi: Buni Ya Nemi CBN Ya Ƙara Wa Jihar Yobe Lokaci

Related

PDP Ta Dage Kan Gudanar Da Taronta Duk Da Sabbin Sharuɗɗan Da Ɓangaren Wike Ya Gindaya
Siyasa

PDP Ta Dage Kan Gudanar Da Taronta Duk Da Sabbin Sharuɗɗan Da Ɓangaren Wike Ya Gindaya

15 hours ago
INEC Ta Amince Da David Mark A Matsayin Shugaban ADC
Manyan Labarai

INEC Ta Amince Da David Mark A Matsayin Shugaban ADC

3 days ago
APC Ce Ke Kai Mana Hari Saboda Siyasa – Malami
Manyan Labarai

APC Ce Ke Kai Mana Hari Saboda Siyasa – Malami

5 days ago
Rikicin NNPP A Kano: Wani Tsagi Ya Soki Korar Abdulmumini Jibrin Kofa
Siyasa

Rikicin NNPP A Kano: Wani Tsagi Ya Soki Korar Abdulmumini Jibrin Kofa

1 week ago
Tsohon Mataimakin Gwamnan Gombe Da Wasu jigogin PDP Sun Koma APC
Siyasa

Tsohon Mataimakin Gwamnan Gombe Da Wasu jigogin PDP Sun Koma APC

1 week ago
Shugaban Kasa Yana Bibiyar Zanga-zangar Matsin Rayuwa – Minista
Siyasa

Ba Abin Da Zai Hana Tinubu Sake Lashe Zaɓe A 2027 – Jigon APC

2 weeks ago
Next Post
Wa’adin Canjin Kudi: Buni Ya Nemi CBN Ya Ƙara Wa Jihar Yobe Lokaci

Wa'adin Canjin Kudi: Buni Ya Nemi CBN Ya Ƙara Wa Jihar Yobe Lokaci

LABARAI MASU NASABA

Dangote Ya Sake Zama Wanda Ya Fi Kowa Kudi A Afrika Karo Na 12

DAPPMAN Ta Soki Matatar Dangote Kan Rage Farashin Man Fetur

September 13, 2025
Yadda Wani Ya Kashe Ƙaninsa, Ya Ɓoye Gawar A Duro

Yadda Wani Ya Kashe Ƙaninsa, Ya Ɓoye Gawar A Duro

September 13, 2025
Madabba’ar Sin Ta Ba Da Gudunmuwar Littattafai Ga Makarantun Koyar Da Sinanci A Nijeriya

Madabba’ar Sin Ta Ba Da Gudunmuwar Littattafai Ga Makarantun Koyar Da Sinanci A Nijeriya

September 13, 2025
An Kaddamar Da Tashar Watsa Labarai Ta CMG A Chengdu

An Kaddamar Da Tashar Watsa Labarai Ta CMG A Chengdu

September 13, 2025
An Gudanar Da Dandalin Tattauna Al’adu Na Kasa Da Kasa Na Golden Panda Na 2025 A Birnin Chengdu

An Gudanar Da Dandalin Tattauna Al’adu Na Kasa Da Kasa Na Golden Panda Na 2025 A Birnin Chengdu

September 13, 2025
An Tsinci Gawar Ɗalibar Jami’ar Taraba A Ɗakin Saurayinta

An Tsinci Gawar Ɗalibar Jami’ar Taraba A Ɗakin Saurayinta

September 13, 2025
Kasar Sin Za Ta Kare Hakkin Kamfanoninta Ciki Har Da Tiktok

Kasar Sin Za Ta Kare Hakkin Kamfanoninta Ciki Har Da Tiktok

September 13, 2025
Aleksandar Vucic: Serbia Na Goyon Bayan Shawarar Kula Da Harkokin Duniya Da Kasar Sin Ta Gabatar

Aleksandar Vucic: Serbia Na Goyon Bayan Shawarar Kula Da Harkokin Duniya Da Kasar Sin Ta Gabatar

September 13, 2025
Etsu Nupe Ginshiƙin Zaman Lafiya Da Haɗin Kai Ne A Nijeriya — Ministan Yaɗa Labarai

Etsu Nupe Ginshiƙin Zaman Lafiya Da Haɗin Kai Ne A Nijeriya — Ministan Yaɗa Labarai

September 13, 2025
Shugaban Rundunar Sojin Sama Ya Buƙaci Ɗaukar Matakin Yaƙi Da Barazanar Tsaro

Shugaban Rundunar Sojin Sama Ya Buƙaci Ɗaukar Matakin Yaƙi Da Barazanar Tsaro

September 13, 2025
Talla

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In

Add New Playlist

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.