Connect with us

Sirrin Iyayen Giji..

Auren Dole!!!

Published

on

SHARAR FAGE……
Kuka take tamkar ran ta zai fita kan gadon ta na amarci mai tsalelen kyau. Na bi ta da kallo cikin tausayi, lokaci guda kuma can cikin zuciyata naji ina yi mata fatan Allah yasa auren dolen da aka yi
ya zamar mata alkhairi kamar na wa. Ta yi kukan ta mai isar ta, sannan na matsa inda take zaune, na zauna tare da dafa ta nace, “Kukan ya isa haka kuma, ki hakuri, ki yi wa iyaye biyayya, ba za ki tabe ba har abada Karimatu”.
Cikin sanyin jiki ta dago ta dube ni tace,”haba Gadatu, Me zai sa Babana ba zai yi min irin auren ki na soyayyah ba?, dubi yadda kike da mijin ki abin sha’awa, yana son ki, kina son sa, Babu abinda Allah bai muku ba cikin rayuwar ku, sai dai ku gode Allah kawai, kuma….”,Hannu nasa na rufe Mata baki batare dana bari ta kai aya ba. Sannan na dube ta duban nutsuwa nace, “Dube ni da kyau nan, Ni din nan da kike gani na nan, gara ma ke kin san mijin da zaki aura, nikuwa lokacin da aka aura min miji na ma ban san shi ba, sai ranar dana je daki na na taba ganin sa”.
Na yi shiru na dakikar lokaci, sannan na nisa na ci gaba, “Bana son mijina, ban saba da shi ba, ina da wanda nake so, amma sbd biyayyar iyaye na hakura, kuma biyayyar yau ita ce ta jawo min wannan albarkar rayuwar, na kuma tsinci kai na da son mijina tamkar rai na. Ki sani a rayuwa babu abinda ya kai bin maganar na gaba riba, Abinda Babba ya hango, yaro ko ya hau Dala da Gwauron Dutse ba zai hango ba”.
Baki ta saki kawai tana kallo na cikin mamakin cewa nima da take sha’awa irin auren na ta dai na tsinci kai na aciki. Sau tari abinda kake ki cikin rayuwa ya kan zama shi ne mafi alkhairi, Yayin da wanda kake so din kan zama akasin alkhairin.
GINSHIQI…….
Auren dole aure ne wanda ya yi shuhura a zamanin baya, duk da a yanzun ma ana yi, amma bai kai yawan na bayan ba. An wa auren lakabi da auren dole ne kawai saboda iyaye ne ke wa yarinya zabin mijin da ya kwanta musu a zuciya, duba da yadda suka ga mijin ya yi inganci ga auren y’ar su. Kaso mafi rinjaye na auren dole da iyaye ke yi wa y’ay’ansu suna yi ne don samawa yaran su miji nagari don samun rayuwa mai dorewa. Yayin da kaso kadan ne ke aurar da yaran su don son abin duniya ko wata biyan bukatar son zuciyar su.
Wani abu da ‘ya’ya suka gaza ganewa shi ne bin umarnin iyaye tabbas wata hanya ce ta samun rayuwa mai inganci, matukar iyayen sun dora auren ne a bisa tafarkin inganci da kallon cancanta.
Mu hadu sati mai zuwa….
Advertisement

labarai

%d bloggers like this: