Ministar Harkokin Jin kai, Agaji da Inganta Rayuwa, Sadiya Farouq ta bayyana cewa ba gaskiya ba ne ikirarin da wasu ke yi cewa wai ba ta rarraba ayyukan ta a dukkan sassan Nijeriya ba, sai wani yanki kadai, sannan kuma wai ba ta yin aikin ta yadda ya kamata.
Ta ce ita ayyukanta ta na gudanar da su ne a kowace jiha a kasar nan da kuma Gundumar Babban Birnin Tarayya.
Ministar ta yi wannan kalami ne yayin maida martani kan Ikirarin Bibi Dogo wanda ya saka talla a jaridar Daily Trust ta ranar Litinin, 9 ga Agusta, 2022 inda ya yi kira ga Shugaba Buhari da ya kore ta saboda wai ba ta yin aikin ta yadda ya kamata.
A sanarwar da mai taimakawa ministar a fagen yada labarai, Nneka Ikem Anibeze ta fitar, ta bayyana cewa a zahiri Dogo, wanda ya ce shi dattijo ne a jam’iyyar PDP a Karamar Hukumar Bauchi, ya yi magana ne a madadin wasu wadanda ke adawa da ministar, wadanda za a iya gane su ta hanyar karairayin da su ke yadawa.
Ta ce ikirarin da ya yi ba gaskiya ba ne ko kadan, kawai ya wawuko shaci-fadi ne a kan ministar da ofishin ta.
Misali, Dogo ya ce wai ministar ta na amfani da dukiyar gwamnati ta na yin “katsalandan” a siyasar Jihar Bauchi, sannan wai ta na yin haka ne domin mara wa siyasar mijin ta baya a takarar zama gwamnan jihar da ya ke yi a ƙarƙashin tutar jam’iyyar APC.
Haka kuma ya ce ministar ba ta yi komai ba wajen taimakon matan jihar ta ta Zamfara.
A cewar Anibeze, manufar wannan mutum wanda bai ma san kakakin jam’iyyar su na yanzu ba, shi da masu ɗaukar nauyin sa, ita ce su yaudari mutane da labaran ƙanzon kurege tare da haifar da tsana da gaba, sannan su ɗauke hankalin ma’aikatar tare da shafa wa aikin ta kashin kaji.
Ta ce in ba domin kada wasu tsiraru su gaskata ƙarairayin sa ba, to da ma’aikatar ba ta ce masa ƙala ba, amma ya zama wajibi a amsa masa don gyara illar da ya ke son kawowa kuma a tabbatar wa da masu ruwa da tsaki da kuma miliyoyin mabuƙata masu amfana da ma’aikatar a faɗin ƙasar nan cewa zargin sa ba gaskiya ba ne.
Ta ce a Arewa-maso-gabas akwai jimillar masu cin moriyar shirin N-Power su 167,412 kuma a cikin su mutum 31,942 ‘yan Bauchi ne, yayin da ‘yan makarantar firamare da ma’aikatar ke ciyarwa a yankin sun kai 1,603,617 waɗanda yara 444,099 daga Bauchi ne.
Na biyu, wannan dattijon ya yi ƙaryar wai mutanen yankin Kudu-maso-gabas su na zargin ministar da nuna masu wariya, wai ba ta kai aikin tallafi a jihohin su ba.
Akasin hakan, a cewar mataimakiyar,
akwai ‘yan makarantar firamare 778,450 da ake ciyarwa, sannan a ƙarƙashin shirin N-Power akwai mutum 136,629 a yankin.
Na uku, ya yi iƙirarin wai sama da masu cin moriyar N-Power su 80,000 ba a biya su kuɗin su na watanni biyar ba.
Ta ce wannan ma ƙarya ce domin mutum 14,021 da ba a biya kuɗin wata biyar ba su ne su ka jawo, domin komfutar tsarin biyan alawus na Gwamnatin Tarayya da ake kira ‘Payment system Government Integrated Financial Management Information System’ (GIFMIS) ita ce ta dakatar da biyan su a watan Maris na 2020 saboda dalilai daban-daban.
Dalilan sun haɗa da: mallakar asusun banki sama da ɗaya, da yadda masu cin moriyar shirin su ke amfani da asusun wajen karɓar kuɗaɗe (na albashi ko alawus) daga hukimomi daban-daban na Gwamnatin Tarayya ko kuma su ma’aikatan dindindin ne ko sun shiga wasu shirye-shiryen na gwamnati.
Ta ba da misali da Jihar Bauchi, inda tsarin GIFMIS ya warware matsalolin mutum 191 masu cin moriyar shirin har an biya su kuma sun fita daga shirin.
Su kuma ‘yan N-Power na rukunin ‘Batch C’ an kasa su gida biyu ne, wato C1 da C2. A cikin Satumba 2021 aka ɗauki ‘yan C1 kuma za su kammala shirin a wannan watan na Agusta 2022 bayan sun cika wa’adin watanni 12 a cikin shirin.
Ta ce babu wata ƙumbiya-ƙumbiya wajen biyan, kawai mutum ya yi amfani da tsarin da gwamnati ta amince da shi wajen biya, wato NASIMS, inda duk wani mai cin moriyar shirin zai iya ganin dalilin da ya sa aka biya shi ko aka ƙi biyan shi, misali saboda ƙin zama ya yi aiki.
Su kuma ‘yan rukunin C2 da aka zaɓa, sun gama tirenin da tantancewar gani da ido ta hanyar abokan aikin ma’aikatar na hukumar NYSC. An fara tura mutum 490,000 aiki a ranar 1 ga Agusta inda za su fara shiga gurbin masu cin moriyar N-Power mutum miliyan ɗaya da Shugaban Ƙasa ya amince a ɗauka.
A ƙarshe, ta tabbatar wa da jama’a da abokan hulɗa cewa wannan ma’aikatar ta na nan ba gudu ba ja da baya wajen sauke nauyin da aka ɗora mata.
Ta ce ta lura da yadda ake ɗaukar nauyin wasu domin su kai wa ma’aikatar da ministar hari a kafafen yaɗa labarai don a ɓata masu suna, amma wannan duk yarfen siyasa ne maras amfani. Saboda haka ba za ta tsorata ba ko a ɗauke mata hankali daga kan turbar da ta ke a kai ta kai wa mabuƙata agajin da su ke buƙata.