Dan Chinan nan da ake zargi da yin kisan gilla ga budurwarsa Ummukulsum Sani Buhari da aka fi sani da Ummita, ya shaida wa kotu cewa bai so masoyiyar tasa ta mutu ba.
Mista Frank Geng Quarong shaida wa alkali haka ne a lokacin da aka sake gurfanar da shi a ranar Alhamis a kotun da ke zamanta a Kano.
- An Yi Bikin Cika Shekaru 60 Da Sin Ta Fara Tura Tawagar Jami’an Lafiya Zuwa Ketare A Zimbabwe
- Mutum 14 Sun Jikkata Yayin Da Magoya PDP Da APC Suka Yi Arangama A Bauchi
A zaman kotun na ranar ranar Alhamis, mai gabatar da kara kuma Kwamishinan Shari’a na Jihar Kano, Batista M. A. Lawan ya tambaye Mista Quwangrong ko shi ya kashe Ummita?
Shi kuma ya amsa da cewa, “Ni ban so ta mutu ba, kuma ba na so na mutu.”
Idan ba a manta ba, a shari’ar baya, Mista Geng Quangorong da ake zargi da zuwa gidan su Ummita ya yi mata kisan gilla, yi ikirarin kashe mata kudi sama da Naira miliyan 100 cewa zata ta aure shi, amma daga baya ta juya masa baya, da ta ga ya tsiyace.
Da yake kare kansa a ranar Alhamis, ya gabatar wa kotun wani bidiyon da ya ce Ummita ce ta turo masa na gidan da take ginawa a Abuja.
Kotun ta sanya bidiyon da kuma wani bidiyon kayan bikin da dan Chinan ya yi ikrarin ya saya wa marigayiyar.
Amma mai gabatar da kara ya tambaye shi dalilin zuwansa gidan su marigayiyar ba tare da an gayyace shi ba, inda ya amsa da cewa dama can ya saba zuwa gidan.
Ya tambaye shi dalilin da bai yi wa mahaifiyar Ummita magana ba a lokacin da ta bude masa gidan, amma ya amsa cewa saboda ba sa fahimtar yaren juna ne.
Game dalilin shigarsa gidan kuwa, amsawa ya yi da cewa ya shiga ne don ya dauki karensa.
Har ila yau an tambayi Mista Geng ko shi ya kashe Ummita? Sai dai amsar wannan tambaya ta gagara, inda ya ce ‘Ni ban so ta mutu ba, kuma ba na so na mutu’.
Daga nan Alkalin Kotun Mai Shari’a Sanusi Ado Ma’aji ya dage shari’ar zuwa ranar 29 da 30 ga watan Maris, 2023 don ci gaba da sauraren shaidun kariya.