Shugaban Kasa Muhammadu Buhari, ya tabbatar da cewa gwamnati za ta tabbatar ‘yan Nijeriya ba su wahala ba ta fuskar kasuwancinsu da kuma samun tsaiko wajen musanya tsofaffin kudi da sabbi a yayin da wa’adin da Babban Bankin Nijeriya (CBN) ya bayar.
Yayin da yake martani game da rahoton dogayen layukan mutanen da ke shafe sa’o’i domin samun musanya tsofaffin kudinsu a bankuna, lamarin da ya janyo suka daga bangarori daban-daban.
- Kasar Sin: An Yi Tafiye-tafiye Sama Da Miliyan 300 A Lokacin Hutun Bikin Bazara
- Kasar Sin Ta Jaddada Muhimmancin Dagewa Nuna Fifiko Ga Ci Gaban Gina Zaman Lafiya
A wata sanarwa da mai magana da yawun shugaban kasa, Malam Garba Shehu ya fitar, shugaba Buhari ya jaddada cewa an fito da batun sauya fasalin kudin ne domin yin maganin mutanen da ke boye kudin haram ba don cutar da talaka ba.
Ya kuma ce hakan zai magance matsalar cin hanci da rashawa da daukar nauyin ta’addanci da satar mutane domin karbar kudin fansa.
Buhari ya kuma ce tsarin zai taimaka wajen karfafa tattalin arzikin kasar nan.
Game da wahalhalun da talakawa ke sha na musanya kudadensu kuwa, shugaba Buhari ya tabbatar da cewa gwamnati za ta yi iya bakin kokarinta domin taimaka musu wajen musanya kudadensu.
Ya kuma jaddada cewa CBN da sauran bankunan kasar nan su kara habaka hanyoyin musanya wa mutane kudadensu domin tabbatar da cewa an musanya wa kowa kudinsa kafin cikar wa’adin.
CBN dai ya saka ranar 31 ga watan Janairu, 2023 a matsayin ranar karshe ta daina amfani da tsofaffin takardun kudi na Naira 200, 500 da kuma 1000.