ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Thursday, July 16, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Taron MDD: Gwamntin Tarayya Za Ta Dauki Nauyin Gudanar Da Makarantar UNESCO A Nijeriya – Minista

by Sulaiman
3 years ago
Tarayya

Ministan Yaɗa Labarai Da Wayar Da Kai, Alhaji Mohammed Idris, ya bayyana ƙudirin Gwamnatin Tarayya na buɗe babbar makarantar koyar da aikin jarida da ilimin labarai ta Hukumar Ilimi, Kimiyya da Al’adu ta Majalisar Ɗinkin Duniya (UNESCO Category 2 Institute for Media and Information Literacy) a Nijeriya ba tare da ɓata lokaci ba.

Ministan ya faɗi haka ne a wajen taron ƙasa da ƙasa na Mataimakin Darakta-Janar mai kula da Yaɗa Labarai na UNESCO, Dakta Tawfik Jelassi, a wani sashe na Babban Taro na 42 na hukumar UNESCO a ranar Talata a Paris, babban birnin ƙasar Faransa.

  • Rashin Tsaro: Za Mu Fara Horar Da Jami’an Sa-Kai Don Tsare Al’ummar Zamfara – Gwamna Lawal
  • Wadanne Damammaki Da Aka Samu Cikin Abubuwan Da Aka Nuna A Karon Farko A Duniya A CIIE?

Wannan alƙawari da Nijeriya ta yi na buɗe wa tare da ɗaukar nauyin makarantar, an yi shi ne tun lokacin da aka yi Makon Aikin Jarida da Yaɗa Labarai na Duniya na UNESCO na shekarar 2022, wanda aka yi a Nijeriya cikin Oktoba 2022, a Abuja, wanda kuma aka rattaba hannu kan ƙudirin aikin a Zama na 216 na Babbar Hukumar Gudanarwar UNESCO, cikin Mayu 2023.

ADVERTISEMENT

Yayin da ya ke ƙara tabbatar da sadaukarwar Nijeriya ga manufofi da burukan UNESCO, Minista Idris ya bayyana cewa duk da yake ƙasar nan ta na shirin sauka daga kujerar ta a Majalisar Ƙasa da Ƙasa ta Shirin Cigaban Harkokin Yaɗa Labarai na Duniya na UNESCO (IPDC), bayan ta shafe shekaru shida a majalisar, to kuma ta na neman zama memba a Majalisar Ƙasa da Ƙasa ta Shirin Samar da Labarai ga Kowa, wato ‘Information for all Programme’ (IFAP).

LABARAI MASU NASABA

Saliba Zai Yi Jinyar Watanni 5 Bayan Raunin Da Ya Samu A Bayansa

Kotu Ta Yanke Wa Wani Hukuncin Ɗaurin Shekara 7 Kan Tallan Wiwi A Kafafen Sada Zumunta

Idris ya sha alwashin cewa, zai tabbatar Nijeriya ta ci moriyar dukkan wasu damarmaki da ke akwai a Sashen Aikin Jarida da Yaɗa Labarai na UNESCO, ciki kuwa har da samar da ƙananan gidajen rediyo na unguwanni, wanda ya na daga cikin tsare-tsaren da UNESCO ta ke ba muhimmanci a yanzu.

Ministan ya kuma bayyana ƙudirinsa na dawo da darajar kafafen yaɗa labarai na gwamnatin Nijeriya, tare da kuma samar da tattaunawar ƙasa gaba ɗaya kan kyawawan ɗabi’u da halayen Nijeriya, a matsayin wani shirin gangamin wayar da kan jama’a da za a yi a duk faɗin ƙasar, wanda ya ce al’amari ne da gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu ta ɗauka da muhimmanci.

Ministan ya gode wa Jakadiya Hajo Sani saboda aiki tuƙuru da ta ke yi na wakiltar burukan Nijeriya a UNESCO, da muhimmiyar rawar da ta taka wajen samar wa Nijeriya damar zama mai masaukin baƙi a Makon Aikin Jarida da Yaɗa Labarai na Duniya na UNESCO na shekarar 2022, da kuma shirye-shiryen da ake yi don ɗaukar nauyin da Nijeriya za ta yi na buɗe babbar makarantar ‘UNESCO MIL Institute’ ta farko a duk duniya.

Da ya ke mayar da jawabi, Mataimakin Darakta-Janar na UNESCO, Dakta Jelassi, ya yaba wa Nijeriya kan babbar rawar da ta ke takawa a UNESCO, sannan ya yi alƙawarin cewa, hukumar za ta ci gaba da mara wa ƙasar baya domin ta ci moriyar dukkan damarmakin da ke akwai na haɓaka ɓangarenta na aikin jarida da yaɗa labarai.

Ya lissafa ayyukan da UNESCO ke aiwatarwa a sassa daban-daban, daga tabbatar da ‘yancin ‘yan jarida a ƙasashen duniya, zuwa tallafawa wajen kafa gidajen rediyo na unguwa, da aikin da ake yi don daidaita ayyukan da ƙasashe ke yi wajen yaƙar baza labaran bogi, da labaran ƙarya da kuma kalaman ɓatanci.

Tun da farko, mai girma Ministan Yaɗa Labarai, Mohammed Idris, ya na cikin ayarin sauran mahalarta taron daga Nijeriya, ciki har da shugaban tafiyar, wato mai girma Ministan Ilimi, Farfesa Tahir Mamman (wanda kuma shi ne Shugaban Hukumar UNESCO ta Ƙasa), da su ka halarci bikin buɗe Babban Taro na 42 na UNESCO.

Tarayya
Sulaiman
+ postsBio
  • Sulaiman
    Binciken CGTN: Amfanar Da Kowa Da Kowa Shi Ne Ainihin Alherin Da Fasahohin Kwaikwayon Tunanin Bil Adama Suka Kawo
  • Sulaiman
    Sin Ta Yi Kira Da A Kafa Tsarin Jagorantar Muhimman Ma’adinai Ga Sauyawa Zuwa Amfani Da Makamashi Mai Tsafta
  • Sulaiman
    Gwamna Dauda Lawal Zai Gabatar Da Jawabi A Taron Ƙasa Da Ƙasa Na Jami’ar FUE Zariya
  • Sulaiman
    Neman Raba-Gari Da Sauran Kasashe Zai Kawo Mummuann Tasiri Ga Bangarorin Da Abin Ya Shafa

MASU ALAKA

Saliba Zai Yi Jinyar Watanni 5 Bayan Raunin Da Ya Samu A Bayansa
Manyan Labarai

Saliba Zai Yi Jinyar Watanni 5 Bayan Raunin Da Ya Samu A Bayansa

July 16, 2026
Kotu Ta Yanke Wa Wani Hukuncin Ɗaurin Shekara 7 Kan Tallan Wiwi A Kafafen Sada Zumunta
Manyan Labarai

Kotu Ta Yanke Wa Wani Hukuncin Ɗaurin Shekara 7 Kan Tallan Wiwi A Kafafen Sada Zumunta

July 16, 2026
Tinubu Yana Zuba Kyawawan Ayyuka A Nijeriya – Ganduje
Manyan Labarai

Ganduje Ya Buƙaci A Yi Siyasar Aƙida Domin Inganta Dimokuraɗiyya A Nijeriya

July 16, 2026
Next Post
NLC Da TUC Sun Rufe Titin Zuwa Filin Jirgin Saman Abuja, Sun Bukaci A Hana Zuwa Imo

NLC Da TUC Sun Rufe Titin Zuwa Filin Jirgin Saman Abuja, Sun Bukaci A Hana Zuwa Imo

LABARAI MASU NASABA

Saliba Zai Yi Jinyar Watanni 5 Bayan Raunin Da Ya Samu A Bayansa

Saliba Zai Yi Jinyar Watanni 5 Bayan Raunin Da Ya Samu A Bayansa

July 16, 2026
Kotu Ta Yanke Wa Wani Hukuncin Ɗaurin Shekara 7 Kan Tallan Wiwi A Kafafen Sada Zumunta

Kotu Ta Yanke Wa Wani Hukuncin Ɗaurin Shekara 7 Kan Tallan Wiwi A Kafafen Sada Zumunta

July 16, 2026
Tinubu Yana Zuba Kyawawan Ayyuka A Nijeriya – Ganduje

Ganduje Ya Buƙaci A Yi Siyasar Aƙida Domin Inganta Dimokuraɗiyya A Nijeriya

July 16, 2026
Binciken CGTN: Amfanar Da Kowa Da Kowa Shi Ne Ainihin Alherin Da Fasahohin Kwaikwayon Tunanin Bil Adama Suka Kawo

Binciken CGTN: Amfanar Da Kowa Da Kowa Shi Ne Ainihin Alherin Da Fasahohin Kwaikwayon Tunanin Bil Adama Suka Kawo

July 15, 2026
Sin Ta Yi Kira Da A Kafa Tsarin Jagorantar Muhimman Ma’adinai Ga Sauyawa Zuwa Amfani Da Makamashi Mai Tsafta

Sin Ta Yi Kira Da A Kafa Tsarin Jagorantar Muhimman Ma’adinai Ga Sauyawa Zuwa Amfani Da Makamashi Mai Tsafta

July 15, 2026
Gwamna Dauda Lawal Zai Gabatar Da Jawabi A Taron Ƙasa Da Ƙasa Na Jami’ar FUE Zariya

Gwamna Dauda Lawal Zai Gabatar Da Jawabi A Taron Ƙasa Da Ƙasa Na Jami’ar FUE Zariya

July 15, 2026
Neman Raba-Gari Da Sauran Kasashe Zai Kawo Mummuann Tasiri Ga Bangarorin Da Abin Ya Shafa

Neman Raba-Gari Da Sauran Kasashe Zai Kawo Mummuann Tasiri Ga Bangarorin Da Abin Ya Shafa

July 15, 2026
Kevin Kelly: AI Na Iya Taimakawa Wajen Cimma Burin “Koyar Da Dalibai Da Kwazonsu”

Kevin Kelly: AI Na Iya Taimakawa Wajen Cimma Burin “Koyar Da Dalibai Da Kwazonsu”

July 15, 2026
Gwamna Yusuf Ya Bai Wa Masu Kula Da Akwatinan Zaɓe Na APC Filaye 1,540 Da Tallafin Miliyan 100

Gwamna Yusuf Ya Bai Wa Masu Kula Da Akwatinan Zaɓe Na APC Filaye 1,540 Da Tallafin Miliyan 100

July 15, 2026
Sabbin Ministoci

Rashin Tsaro: Majalisar Dattawa Ta Bukaci A Tura Ƙarin Sojoji da ’Yansanda Zuwa Benuwe

July 15, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.