Kwamared Hajiya Rukayya Abdurrahaman wadda akafi sani da Uwar Marayu, Shugabar KungiyarTallafa Wa Marayu da Zawarawa ta Jihar Kano, ‘Yar Gwagwarmaya Mai kishin Tallafa wa Marayu da iyaye Mata musamman Zawarawa a Jihar Kano.
A tattaunawar ta da Wakilinmu a Kano Abdullahi Muhammad Sheka ta bayyana tsananin damuwar da ta ke tsintar kanta a ciki idan ta tuna irin halin da Marayu da Mata Zawara ke ciki a irin halin rayuwar da ake fama da ita a wannan lokaci, sannan ta bayyana shirin wannan Gidauniya na yunkurin samar da tallafi ga Marayu da sauran masu bukata ta musamman. Ga dai yadda tattaunawar ta Kasance.
Za mu so mu san wacce muke tare da ita a halin yanzu?
Alhamdulillahi kamar yadda aka sani ni dai, sunana Kwamared Hajiya Rukayya Abdurrahaman haifaffiyar Unguwar Gwagwarwa, Karamar Hukumar Nasarawa a Jihar Kano na yi karatun addinin musamman Alkur’ani, ilimin addini da na zamani gwargwadon ikon, yanzu haka ina ci gaba karatun digiri har da digirgir a fannin tsimi da tanadi a Jami’ar Bayero da ke Kano, sannan kuma ni ce Shugabar Kungiyar Tallafawa Marayu da Zawarawa da cigabansu ta Jihar Kano a halin yanzu.
Ganin ke Mace ce kuma kika rungumi wannan tsari na taimakon Marayu da Zawarawa, shin ko me ya ja hankalinki zuwa wannan aikin alhairi?
Kamar yadda na ambata tun a cikin gabatarwar da na yi, na taso a cikin al’umma da ke fama da irin wannan matsala, sannan karatun addini da na yi ya ba ni damar fahimtar muhimmancin tallafa wa Marayu da kuma gagarumin kalubalen da ke addabar wadanda suka tsinci kai a irin wannan hali, babban tashin hankalin shi ne yadda matsalar maraici ke jefa kananan yara harkar shaye-shaye, sace-sace da barace-barace wanda hakan na zubar da kimar addinin mu na Musulunci da al’adunmu. Wannan shi ne abinda kullum idan na tuna ke hana ni runtsawa.
Kwamared yaushe aka kafa wannan kungiya?
Mun kafa wannan kungiya shekaru biyar da suka gabata karkashin Jagorancin Galadiman Kano Alhaji Abbas Sunusi, tare da gudunmawar wasu mashuhuran mutane masu zuciyar taimakon al’umma wanda zuwa yanzu muna da cibiyoyi guda biyu, daya na Unguwar Hotoro gudan kuma na Unguwar Kabuga duk a Jihar Kano
Mene ne ayyukan da kuka fi mayar da hankali akansu?
Alhamdulillahi kamar yadda na ambata akwai taimaka wa Marayu wadanda muke koya masu sana’o’in dogaro da kai, mayar da su Makarantu, sannan da daukar nauyin karatun nasu, hakazalika muna bibiyar lafiyarsu, tare da biya masu kudaden maganunguna. Yanzu haka muna da sama da Marayu 100 da duk mako muke haduwa dasu ana koya masu sana’a tare da koya masu karatun addini da na zamani, sannan muna aamar masu da dan abin sawa a bakin salati.
Wanne tanadi wannan kungiya ta yi wa Mata Zawarawa?
Gaskiya lamarin Zawarawa shima lamari ne mai zaman kansa, domin wasu matan mutuwa aka yi aka barsu da Marayu kenan aiki biyu ya samu mace guda ga zawarci ga kula da marayun da aka bar Mata. Wannan tasa daga kafuwar wannan kungiya zuwa yau mun taimakawa zawa sama da dubu biyar, wadanda muke Koyawa sana’u iri daban daban, Kama daga dinki, tursruksn wuta, girke girke, kula rayuwarsu domin gudun afkawa ciki wata mummunar dabi’a, sannan da tallafawa wadanda suka samu mazajen aure tare da bibiyar su domin ganin yadda suke ci gaba kula da sana’o’in da aka koya masu.
Ta yaya wannan kungiya ke samun kudeden gudanar da harkokin ta?
Muna samun tallafi daga hannun wasu mutanen kirki da wasu da bama da son a ambata sunansu, amma dai babu shakka uban wannan kungiya Galadiman Kano da Kwamishinan yada labaran Jihar Kano Kwamared Myhammad Garba babu shakka suna yin bakin kokari kwari da gaske.
Kungiya irin wannan na bukatar matsuguni Wanda zata ci gaba lura da kula da wadannan marayu, shin ko ita wannan kungiyar nada nata matsuguni na dindin?
“Kaji inda gizo ke sakar” yanzu haka maganar da ake amma bamu umarnin hada kayanmu domin ficewa daga gidan da muke gudanar da wannan aikin alhairi za su sayar da kayansu, kuma babbar matsalar ita ce idan aka tashe mu ba mu san inda kuma zamu nufa ba, kenan kaga wannan aikin ya gamu da tasgaro wanda hakan ka iya takaita amfanin da al’umma ke samu karkashin ayyukan wannan kungiya.
Wane kira za ki yi ga mahukunta da masu hannu da shuni domin shigowa cikin wannan aiki alhairi?
Babban kiranmu ga mahukunta da sauran masu bukatar zuba jarinsu a inda ba gara ba zago shi ne, lallai su yi kokarin sayawa wannan kungiya matsuguni domin amfanin marayu, sannan bisa yadda muke fadi tashi a fadin kananan Hukumomin Jihar Kano 44, akwai bukatar samun motar da zamu ci gaba da tiri tiri da wadannan marayu tare da bibiyar Zawarawan da aka koyawa sana’ar dogaro da kai domin ganin suna ci gaba amfanarta, Wanda rashin abin hawa na ragewa aikin namu armashi.
Mene fatan ki na karshe?
Fatan na karshe cikawa da imani, kuma tare da rokon Allah ya karbi wannan kyakkyawan aiki, sannan wadanda ke bayar da gudunmawa suma Allah ya hada mu a ladan.
Mun gode
Nima na gode