Ba Sauran Jam’iyya A Kano, Sai Gandujiyya – Fairus Ibrahim

Honarabul Fairus Ibrahin Hassan shi ne Mai bai wa Gwamnan Kano Dakta Abdullahi Umar Ganduje Shawara Kan Harkokin Ma’adanai, guda cikin matasan ‘yan siyasa da Karansu Kano ya kai tsaiko, matashin da kullum ke kokarin dinke duk wata baraka musamman a karamar Hukumar sa Kumbotso. A Tattaunawarsa da Wakilinmu  A Kano Abdullahi Muhammad Sheka, Fairus Ibrahim Hassan ya bayyana yadda jihar Kano yanzu ta zama tsintsiya madaurin ki daya ta fuskar ci gaban da aka samu, wanda yace yanzu haka jihar Kano kafatan Ganduje ake yi ba sauran wata Jam’iyya ko kungiya. Sannan kuma ya yi karin hake kan sakamakon taron da ya gudana kan batun yi wa harkokin ma’adani kallon tsanaki tare da bujiro da hanyoyin fara amfana da albarkatun kasar da ke shimfide a Jihar Kano. Ga dai yadda tattaunawar ta Kasance.

Idan aka yi la’akari da yadda Gwamnatin Ganduje ke kanfato ayyuka a Jihar Kano, shin anya kuwa zaku iya kammala su kafin karshen wannan zangon da kuke ciki?

Alhamdulillahi da sunan Allah mai yawan rahama mai yawan jinkai, ni ina mamakin irin wannan tambaya da ‘yan Jarida kuke yi, ai ko makaho ya san al’amarin Ganduje ikon Allah ne. ku na ina akayi ta kwazazton cewar an barwa wannan Gwamnatin makudan kudade a lalitar gwamnati a lokacin bikin mika mulki, kun manta da cewar da aka yi cewa ba’a bin gwamnatin bashin ko sisin kobo, ko kuwa mantawa kuka yi da yadda aka jidi ‘ya’yan al’umma aka kaisu kasashen waje da sunan karatu aka bar wasu cikin talauci da damuwar gaske.

Wadanann su ne abubuwa da mai hankali ya kamata ya fara dubawa, amma kamar yadda ake ganin sakamakon kyakkyawar niyyar Gwamna Ganduje ya sa tun zuwan wannan Gwamnati da farko dai bata taba batan dabon biyan al’bashi ba, sannan kuma itace gwamnati daya tilo da ta kau da kai tare da ci gaba da ayyukan da tsohuwar gwamnati ta faro wanda wasu aikace aikacen ko kaso 5 daga cikin 100 ba akai ba Gwamnatin ta kare, misali dubi aikin gadar sama da ake yi a titin Murtala Muhammad wanda ya ratsa kasuwar Asabon gari har zuwa Kano Club, amma Gwamna ganduje duk ya san an wawashe kasha 1o cikin 100, tunda fari haka ya ci gaba da aikin wanda yanzu maganar karewa ake.

Saboda haka maganar za a iya gama aiki ko ba za a iya gamawa wannan bai ma taso ba, domin wani ma ya yi rawa balle dan Makada, muna tabbatarwa da Jama’a cewar da yardar Allah duk aikin da Gwamnatin Ganduje ya faro sai an gama shi domin yawancin ayyukan da ake bayarwa ba’a farawa sai an aje kudadensu, zan baka misali da katafaren aikin Gadar Kasar da aka fara yanzu shatale talen Dangi zuwa Titin zuwa Gidan Zoo wanda zai lakume Naira Biliyon hudu, wannan aiki ne da ba irinsa wanda zai amfani al’umma masu yawan gaske, kuma kamar yadda aka sani wannan wuri ya na da  matukar amfani ga al’ummar Jihar Kano.

 

Ofishin ka ne ya jagoranci gabatar da taron nazari kan ma’adanai da aka gudanar a Jihar Kano, shin ko mene dalilin shirya wannan taro?

Alhamdulillahi kamar yadda aka sani aikin wannan ofsi ne dubawa tare da zakulo ma’adanan da Allah ya horewa Jihar Kano, saboda haka muka shirya wannan taro domin gayyatato masana tare masu sha’awar zuba jari a irin wannan harka. Kamar yadda aka sani Allah cikin ikonsa ya shimfida ma’adanai masu yawan gaske a karkashin wannan Jiha ta mu mai albarka, misali idan ka dauki wasu Kananan hukumomi kamar guda bakwai wanda suka hada da Doguwa wanda riruwai ke cikinta, Kabo, Karaye, Danbatta Tsanyawa da sauransu, wuraren da Allah ya albarka ce su da arziki mai tarin yawa kwance a karkashin kasa. Saboda haka Gwamnatin Ganduje ta damu kwarai da yadda ake yiwa al’ummar arewacin kasar nan kallon cima zaune duk da cewar tarihi ya tabbata cewa da kudin gyada, auduga da fata aka samu zarafin hakar man fetur din da yanzu wasu ke kumaji dashi. Wannan tasa Gwamna Ganduje amincewa da yin nazari tare da gabatar da shawarwarin da za’a bi wajen fara hakar wadannan ma’adanai domin cin gajiyar sa. kuma alhamdulillahi an gudanar  Wannan taro  tsawon kwanaki uku, tare da samun cikakkiyar Nasara.

 

Shin ko wane sakamako aka fara gani bayan kammala taron wanda ke nuna cewa akwai alamar kwalliya na iya biyan kudin Sabulu?

Gaskiya muna yiwa Allah godiya domin tun ba ‘aje ko ina ba yanzu haka har wasu mutane daga kasashen waje sun fara gabatar da sha’awar su na zuba jari a wannan harka, kuma a shirye mai girma Gwamna yake da zaunawa dasu domin tattauna yadda za’a kulla yarjejiniyar domin ganin al’umma Kano sun fara amfana da wadanan albarkatun kasa da ke kwance a Jihar Kano. Bayan wannan kuma ita kanta jihar Kano muna shirin gabatar da shawarar fara hakar wadanann ma’adanai domin fitar dasu zuwa kasashen waje, wanda muna kyautata zaton bisa ga yadda taron ya nuna kwalliya zata biya kudin Sabulu.

Yanzu haka ina tabbatar maka da cewa akwai Kamfanonin Kasashen waje guda uku wanda suka nuna sha’awar su ta zuba jari a wannan harka, kuma tuni an fara tattaunawa dasu domin shiga cikin yarjejiniyar fahimtar juna tsakanin Jihar Kano da wadanan Kamfanoni. Kuma alhamdulillahi kasancewar Gwamna Ganduje kullum aniyar sa itace ganin Jihar Kano ta fita daga cikin jihohin da ake yiwa gorin dogaro da man Fetur, kuma Gwamna zai yi duk mai yiwuwa domin tabbatar da ganin an samar da tsari mai dorewa domin ci gajiyar shirin hakar ma’adanan da Allah ya horewa Jihar Kano.

 

Kana cikin matasan ‘yan siyasa da suke sahun gaba wajen ganin an kare manufofin Gwamna Ganduje, kuma abaya an shajin yadda ake ya mutsa gashin baki tsakanin fulogan APC  a Karamar Hukumar Kumbotso, amma yanzu anji shiru ko mene ya faru?

Alhamdulillahi yanzu ba Kumbotso ba Jihar Kano ma gaba daya kwata ba sauran wata Jam’iyya ko Kungiya Ganduje ake Sak, saboda haka muma a Kumbotso tuni aka dinke wannan barakar yanzu ba sauran wani motsi, Ganduje kawai muke kuma shi za’a zaba shekarar zabe mai zuwa. Muna yiwa Allah godiya iyayen Jam’iyya a Kumbotso suna yin duk mai yuwuwa wajen tabbatar da kimar Gwaman Ganduje, musamman ganin yadda ake kwararo ayyukan ci gaba a Karamar Hukumar Kumbotso.

 

Ya Kuke kallon takarar Gwamna Ganduje a kakar zabe mai zuwa  ta shekara ta 2019?

Alhamdulillahi batun takarar Gwamna Ganduje a shekara ta 2019 kamar da kasa inji Mai ciwon ido, kuma muna tabbatarwa da jama’a cewar Gwamna Ganduje ya zama wajibi ya amsa kiran  al’ummar Kanp, jama’ar Kano basu da wani gwani da ya wuce Gwamna Ganduje, ina tabbatar maka ayyukan da Gwamna Ganduje ke aiwatarwa a Kano ko hasidin iza Hasada ya san ko ba’a gwada ba linzami ya fi karfin bakin kaza. Dubi Gadojin Kasa guda uku da ake gudanarwa a birnin Kano wanda babu irinsu a fadin tarayyar Najeriya.

Wannan da ma sauran  ayyukan da yanzu al’umma ke ci gaba da godiya su ka sa jama’a ba suda wani zabi da ya wuce Gwamna Ganduje, kuma ba alfahari muke ba ba wani gwamna a kasar nan  da ya kai Ganduje cin nasara a cikin wadanan shekaru uku masu albarka, kamar yadda Jam’iyyar APC  ta zama fitilar dake haske kyakkyawar Makomar Najeriya.

 

Mene sakon ka na karshe?

Babban sakon mu ga jama’ar Kano shi ne a ci gaba da baiwa wanann Gwamnati dukkan hadin kai da goyon bayan da ake bukata, sannan kuma  kamar yadda yanzu gwamnatin Ganduje ta mayar  da hankali ta fuskar taimakon jama’a, tallafawa mata, ingatan harkokin rayuwar yara da kuma harkokin ilimi. Bayan haka muna jadadda godiyar mu tare da amincewa da jagorancin da shugabannin Jam’iyya a Jihar Kano ke yiwa ‘yan Jam’iyyar APC  a Jihar Kano wanda hakan ya haifar da irin ci gaban da ake alfahari dashi. Muna rokon jama’a kowa ya kara karkade kuri’unsa domin yiwa shugaban kasa Muhammad Buhari da aminisa Gwamna Ganduje luguden kuri’u alokacin zaben shekara t 2019.

 

Mun gode kwarai

Ni ma ina godiya

 

Exit mobile version