“Na dauki rubutu wani babban al’amari a gare ni, kuma rubutu baiwa ce da ba yadda za a yi haka kawai ka ce za ka yi rubutu ba tare da Allah ya baka wannan baiwar ba”, cewar KHADIJA SALEH kenan wacce aka fi sani da JIKAR HAJIYA. Daya ce daga cikin marubuta masu tasowa na yanazar gizo a yanzu. Ta kuma bayyana wa masu karatu babban kalubalen da ta fuskanta bayan fara rubutunta wanda ya zame mata karfen kafa cikin zuciya, a duk lokacin da ta tuna. Ga dai tattaunawar tare da PRINCESS FATIMA ZARAH MAZADU Kamar haka:
Da farko za ki fadawa masu karatu cikakken sunanki tare da sunan da aka fi saninki da shi?
Sunana Khadija Saleh, wacce aka fi sani da Jikar Hajiya.
Ko za ki fadawa masu karatu dan takaitaccen tarihinki?
To Alhamdullah ni dai haifafiyar Azare ce jihar Bauchi, Alhaji Saleh Mai Cassette Sarkin Fulani shi ne mahaifina. Na yi karatu anan Azare tun daga firamare J I S, SSC zuwa deploma, kuma na yi shi ne a Potiskum, ina tare da kakata Hajiya Laraba wadda kusan a tare da ita na karasa rayuwata, mahaifina ya rasu shekara ta 2014 a sanadiyar wutar Nepa.
Me ya ja hankalinki ki ka tsunduma fannin rubutu?
To abin da ya ja hankali na na fara rubutu shi ne, da fari rubutun birge ni ya ke daga baya sai na fahimci rubutu wata muhimmiyar hanya ce mafi saurin isar da sako.
Ya gwagwarmayar farawar ya kasance?
Uhmm, wai! gaskiya kam, an sha gwagwarmaya dan lokacn dana fara sai kuma na zo nake kallon kamar ba zan iya ba, sai na ce na hakura ba zan iya ba, bayan kwana biyu kuma sai dai na sake cigaba da yi, a haka dai har na fara gogewa.
Lokacin da za ki fara rubutu, shin kin sanar da mahaifiyarki ko kuwa kin fara ne kawai?
To a gaskiya na sanar da mahaifiyata da babban yayana, mahaifiyata ta sanya min albarka kwarai ta yi min fatan nasara, dan idan ban manta ba har ce min ta yi to ita tay aya za ta dinga sauraran littafaina tunda ba iya tsayawa karantawa za ta yi ba, har tana ce min sai dai na dinga karanta mata ‘some time’ ina mata dariya ma.
Kamar wane bangare ki ka fi maida hankali a kai wajen yin rubutu?
Gaskiya hankali na ya fi karkata ne wajen zakulo labarai da suka shafi rikicin rayuwa, rikicin Soyaya, kalubalen rayuwa rayuwar mu a yau, rayuwar aure a wannan zamanin.
Za ki yi shekara nawa da fara rubutu?
To zuwa yanzu dai shekara biyar kenan.
Kin rubuta labarin sun kai kamar guda nawa?
To zuwa yanzu dai sun kai kamar guda 7.
Ko za ki iya fadawa masu karatu sunayen labaran da ki ka rubuta?
To Alhamdullah Adadin su ne kamar haka; A dalilin Matar Uba, Na ‘Yar Fulani, Alhaji Na Babyna, Maryamu Dilaliya, Fadila MD, Masoya Uku, Safna Sad Story. Su ne littafan dana rubuta wato guda bakwai kenan.
Wane labari ne cikin labaranki ya zamo bakandamiyarki, kuma me ya sa?
To a gaskiya wanda ya zamo bakandamiyata shi ne Na ‘Yar Fulani. To ya kasance abin tausayi ne ainun saboda ya kasance akan maraici ne kuma kaluballen da wasu ‘ya’yan suke fuskanta bayan rasa iyayensu.
Wane labari ne ya fi baki wahala wajen rubutawa, kuma me ya sa?
Eh! to, MASOYA UKU gaskiya na sha wahala akan wannan rubutun, wato abin da ya sa rikici ne na soyayya, mijin farko da kuma me neman auren akaro na biyu da kuma wadda ya sha alwashin sai ya aure ta muddiin yana numfashi kode su duka ukun kowa ya rasa ta daya dan kasuwa ne biyu kuma sojoji ne.
Kin taba buga littafi?
Gaskiya ban buga ko guda ba, kuma ban taba tunanin bugawa anan gaba ba.
Wacce irin nasara ki ka samu game da rubutu?
To gaskiya na samu nasara, nasara ta farko shi ne isar da sakon da nayi ga al’umma, na biyu kuma al’ummar da suka karbi sakon har suka nuna min sun ji dadin wannan kuma sun amfana da sakona har ma suna yi min fatan alkhairi da godiya, a gaskiya abun yana yi min dadi.
Ko akwai wani kalubale da ki ka taba fuskanta game da rubutu?
Hmmm tom, wai ta malam bahaushe ya ce “tone-tone ba shi da amfani”, a gaskiya na fuskanci kalubale daga wasu a cikin wadanda muke kamar ‘yan’uwan juna, bayan na fara rubutu ne kuma sai muka kasa fahimtar juna, na fuskanci cin mutunci da kazaman kalamai daga wasu mutane, abin da har yau ya ke taba min zuciya duk lokacin da zan tuna hakan, a lokacin sai da na ajiye rubutu na ce in dai saboda rubutu ne ake min duka wannan to na hakura na daina, sai da nayi shekara kusan biyu bana rubutu daga baya kuma kungiya ta bukaci na dawo na ci gaba da aiki na.
Ya ki ka dauki rubutu a wajenki?
Na dauki rubutu wani babban al’amari a gare ni, kuma sannan rubutu baiwa ce ba yadda za a yi haka kawai ki ce za ki yi rubutu ba tare da Allah ya baki wannan baiwar ba.
Mene ne babban burinki na gaba game da rubutu?
A gaskiya babban burina shi ne na zama gwana kuma shahariyar marubuciyar da duniyar marubuta watarana za ta yi alfahari da ni da kasata bakidaya.
Wane abu ne ya taba faruwa da ke na farin ciki ko akasin haka wanda ba za ki manta da shi ba?
Eh! gaskiya na samu duka biyun na samu bacin rai a game da rubutu haka kuma na samu yabo akan rubutu na nagode Allah na.
Wane abu ne idan ki ka tuna shi ki ke jin dadi?
Eh! to idan na tuna na rubuta abu me amfani kuma an karanta an yi amfani da shi har ma an samun albarka hakan yana sanya ni nishadi da jin dadi.
Bayan rubutu kina sana’a?
Eh! bayan rubutu ina sana’ar dinki, kuma ina sayar da kayan sanyi.
Kamar da wane lokaci ki ka fi jin dadin yin rubutu?
Na fi jin dadin sa da dare wuraren 10:00 idan kowa ya kwanta, ko bayan sallar asuba kafin a fara hayaniya.
Me za ki ce da makaranta labaranki?
Gaisuwa tare da fatan alkhairi kuma zan sanar da su ina matukar alfahari da su.
Ko kinada wadanda za ki gaisar?
Eh! na gaisawa ga nahaifiyata kakata Hajiya Laraba (Mai fura Potiskum) Sadiya Zakariyya (Mrs Zarks) Yusuf B Saleh Alhaji Usman Porthcourt.