Kociyan kungiyar kwallon kafa ta Liverpool, Jurgen Klopp, ya bayyana cewa kungiyar ba zata sayar da dan wasanta Muhammad Salah ba duk da rade radin da ake na cewa dan kasar Masar din yana son barin kasar Ingila s karshen kakar wasa ta bana.
A karshen satin daya gabata ne dan wasan gaban na Liverpool, ya bayyana yiwuwar raba gari da tawagar ta sa nan gaba kadan, dai dai lokacin da kungiyar ke komawa matsayin jagorar shirin lashe gasar Firimiya karo na biyu a jere.
Yayin wata zantawar abokin wasan Salah dan Masar a tawagar kasa da jaridar wasanni ta AS Mohamed Aboutrika ya ce ita kanta Liverpool na kokarin sayar da dan wasan mafi zura mata kwallo a raga a halin yanzu, ko da ya ke tuni kocin Liverpool din Jurgen Klopp ya musanta batun.
Aboutrika ya ce Muhammad Salah mai shekaru 28 a duniya ya fusata matuka da yadda kungiyar ta ki bashi mukamin Kyaftin yayin wasansu da kungiyar Midtjylland karkashin wasannin cin kofin zakarun Turai na Champions League maimakon haka sai ta bai wa abokin wasansa Trent Aledandre Arnold jagorancin saboda rashin Jordan Henderson.
Matukar dai ta tabbata Salah zai raba gari da Liverpool zai zama babban gibi ga kungiyar wanda ke kokarin sake dage kofin Firimiya a karo na biyu duk da cewa akwai kungiyoyi da dama da suke bibiyar bayan Liverpool kamar Tottenham da Chelsea da kuma Manchester United.
Sai dai Klopp, wanda yayi hira da manema labarai bayan wasan da kungiyarsa ta Liverpool ta samu nasara daci 7-0 akan kungiyar Crystal Palace, ya bayyana cewa Salah zai ci gaba da zaman kungiyar kuma ba zasu sayar dashi ba akan kowanne farashi.
Zuwa yanzu dai kungiyar kwallon kafa ta Real Madrid ce ke kan gaba a jerin kungiyoyin da suka jima suna farautar dan wasan, kuma dama shi kansa dan wasan masoyin Real Madrid ne tun yana karamin yaro.
Amma kuma banda Real Madrid kungiyar kwallon kafa ta Barcelona tana ganin Salah ne zai iya maye mata gurbin Leonel Messi a kungiyar idan har Messi ya bar kungiyar a kakar wasa mai zuwa kuma shugabannin na Barcelona sun fara tunanin yin Magana da wakikin dan wasa Salah da kungiyar Liverpool akan ko za su sayar mu su da dan wasan wanda ya koma Liverpool daga kungiyar Roma.