Kungiyar masu hakar ma’adinan ta kasa reshen Jihar Neja ta bayyana cewa ba wani dan kungiya da za a yi wa rajistan zama cikakken dan kungiya sai wanda ya mallaki katin zabe.
Shugaban kwamitin tantance ‘ya’yan kungiyar kuma mataimakin shugaban kungiyar na jiha, Alhaji Babangida Sani Mudi ne ya bayyana hakan lokacin da yake amsa tambayoyin manema labarai a Minna.
Alhaji Babangida ya ci gaba da cewar gangamin wayar da kan jama’a kan muhimmancin mallakar katin zabe bai tsaya kan hukumar zabe ba kawai, kowani dan kasa nagari akwai bukatar ya karfafa gwiwar hukumar domin ganin kowa ya mallaki katin zabe.
Ya shawarci sauran kungiyoyi da su dauki irin wannan salon wajen tantance ‘ya’yan kungiyarsu ta yadda ba za a bar su a baya na ganin kasar nan ta ci gaba. Ya ce tantance ‘ya’yan kungiyar ta ba su damar sanin adadin ‘ya’yanta da kuma samun cikakken bayani kan dan kungiya.
Mataimakin shugaban kungiyar ya nisanta ‘ya’yan kungiyar bisa zargin su da shiga cikin ‘yan ta’adda, ya ce a cikin kowani gungun jama’a akwai nagari da kuma bata-gari, amma yana da tabbacin dukkanin mutumin da suka tantance a matsayin mambansu, to mutumin kirki ne.