Gwamnan Dauda Lawal na jihar Zamfara, ya jaddada aniyar gwamnatinsa na kauracewa duk wani batun sulhu da barayi a fadin Jihar Zamfara.
Gwamnan ya bayyana haka ne a yayin da ya halarci taron wa’azi na mako-mako da aka saba gudanarwa a Gusau, inda ya hori Malaman Addini da su kasance masu riko da gaskiya.
- Yadda Kwankwaso Da Abba Suka Jagoranci Auren Gatan Mutum 1,800 A Kano
- Nijeriya Za Ta Fara Fitar Da Man Fetur A 2024 —Kyari
Wata takardar sanarwar manema labarai da mai magana da yawun gwamnan, Sulaiman Bala Idris ya fitar, ta ce wannan taron wa’azin mako an kwashe shekaru ana gudanar da shi, kuma wannan shi ne karo na 1,179.
Ya kara da cewa, gwamnan ya yi kira ga dukkanin shugabannin bangarorin al’umma da su kasance masu gaskiya a dukkanin al’amuransu, tare kuma da yawaita addu’ar wanzuwar zaman lafiya a Jihar.
Sanarwar ta ci gaba da cewa: “Gwamna Dauda Lawal, a yayin da yake jawabi a wurin taron wa’azin mako a Gusau, ya bayyana irin hatsarin da yake tattare da yin sulhu da ‘yan bindiga, inda ya ce, babu abin da sulhun zai haifar sai karin karfi a gare su, tare da ci gaba da jefa al’umma cikin hatsari.
“Ya bayyana cewa dole ne a fuskanci gaskiya, domin kuwa wadannan lalatattun sun nuna cewa ba wai sulhun suke son yi da gaske ba, saboda sun kasance masu saba alkawari. Babu abin da ya rage face a durfafe su da karfin tsiya.
“Gwamna Lawal ya kuma yi kira ga shugabanni, sarakuna da malamai da su rika fadin gaskiya komi dacinta, ba tare da la’akari da wa ta shafa ba, komi dadi ko rashin dadinta.
“Ya yi kira ga shugabannin siyasa da al’umma da su muhimmanta lamarin tsaron jihar gaba da siyasa, domin zaman lafiyan Zamfara shi ne gaba da komi.”
Tun farko dai, a nashi lakcar, shugaban Kwamitin Zakka da Wakafi na Jihar Zamfara, Sheikh Ahmad Umar Kanoma, ya yi dogon jawabi a kan muhimmanci sulhu, inda ya kawo sharudan da addinin musulunci ya gindaya wurin yin sulhu, da kuma yanayin da bai yiwuwa a yi sulhu a addinance.