- Gwamna Yari Ya Kafa Kwamitin Sasantawa
Daga Hussaini Baba, Gusau
A wata sabuwa, gamayyar kungiyoyin kwadago na jihar Zamfara sun bayar da umarnin fara yajin aki na gama-gari a fadin jihar.
Shugaban kungiyar kwadago na jihar Zamfara (NLC) Kwamared Bashir Mafara ne ya bayyana matsayar kungiyar na fara yajin aiki daga jiya Litinin 11 ga watan Satumban 2017. Kuma a jiya Talata 12 ga watan Satumban 2017 ne ilahirin ma’aikatan jihar Zamfara suka amsa kiran kungiyar.
Kwamared Mafara ya bayyana cewa “Makonni uku da suka gabata ne mu ka ba gwamnatin jihar Zamfara wa’adin biyan hakkokinmu na karin albashi, biyan kudaden sallama, da kuma kudaden karin girma, wato (TSS, CONPOCASS da CONTEDISS) da dai sauran hakkokin ma’aikata. Duk wadannan hakkokin namu da wa’adin da muka dauka gwamnati ta yi kunnen uwar shegu damu.”
Haka kuma Kwamared din ya zargi gwamnatin jihar da biyan albashin da ta ga dama, musamman ma na malaman Firamare da kuma ma’aikatan kananan hukumomi. Kungiyar ‘yan kwadagon ta koka da cewa akwai ma’aikatan da ke amsan naira dubu 7,500 da dubu 8,000 a matsayin albashi.
Shugaban kungiyar kwadagon ya ce, suna ci gaba da tattaunawa da bangaren gwamnati, wanda sakataren gwamnatin jihar Zamfara, Abdullahi Shinkafi ke jagoranta. Don a shawo kan lamarin. Sai dai shugaban kungiyar kwadagon ya umurci dukkan ma’aikata a fadin jihar da su kauracewa wuraren ayyukansu.
Mai magana da yawun gwamnan jihar Zamfara, Ibrahim Dosara ya bayyanawa jaridar LEADERSHIP A Yau cewa tun a farkon lamarin gwamnan jihar Zamfara, Abdul’aziz Yari ya zauna da kungiyar ‘yan kwadagon, inda ya fadi musu cewa akwai matsalar aringizo a cikin albashin jihar, wanda kuma ya wuce misali. Don haka yana son yin bincike domin tantance ingantaccen adadin ma’aikata na kananan hukumomi da ma’aikatan jiha. Idan kuma ‘yan kwadagon suna da wannan adadin su kawo masa.
“Gwamna na jiran kwamitin da ya kafa da ya bashi hakikanin adadin ma’aikatan jihar Zamfara. Akwai kwamitin da gwamna ya kafa domin a saurari korafinsu, domin a yi sulhu, wanda sakataren gwamnati ke jagoranta.
“Sannan akwai kwamiti na bin diddigi da son sanin hakikanin adadin ma’aikatan jihar. Tuni kuma wannan kwamiti har ya mika sharar fage na rahotonsa. Kuma rahotonsa ya bayyana cewa ana ninka biyan albashin ma’aikatan da ake dasu a jihar Zamfara. Wanda shi ne Gwamna yake so a fito mishi da sahihin jadawali, wanda dashi zai aiwatar da bukatar ‘yan