Babban Taron APC: Gwamnonin Jam’iyyar Sun Dage A Kan Fabarairu

APC JAMA’A

Daga Sulaiman Ibrahim,

Gwamnonin da aka zaba a karkashin jam’iyyar APC mai mulki a Nijeriya sun yi taro a daren Lahadi inda suka yanke shawarar cewa dole ne a gudanar da babban taron jam’iyyar a watan Fabarairu.

Jam’iyyar APC ta kasa gudanar da babban taronta da kuma zaben sabbin shugabanninta na kasa tun bayan da ta dakatar da tsohon shugabanta Adams Oshiomhole a shekarar 2020.

Jam’iyyar dai ta kasance karkashin jagorancin kwamitin riko wanda gwamnan jihar Yobe, Mai Mala Buni ke jagoranta.

A taron da suka yi a ranar Lahadi, wata kungiyar gwamnonin APC ta Progressive Governors Forum (PGF) ta bayar da tabbacin cewa za a gudanar da babban taron jam’iyyar na kasa a watan Fabarairu.

Gwamna Atiku Bagudu na Kebbi kuma shugaban kungiyar PGF ya bada wannan tabbacin a lokacin da yake zantawa da manema labarai a karshen taron da suka yi a daren Lahadi a Abuja.

Exit mobile version