Connect with us

SIYASA

Babban Taron APC: Sama Da ’Yan Takara 170 Suke Neman mukaman Kwamitin Zartaswa

Published

on

Sama da ‘yan Jam’iyyar APC 170 ne suke hankoron kasance wa zababbu a kwamitin gudanarwar Jam’iyyar da kuma wasu manyan mukamanta na kasa, kamar yadda wani jami’in Jam’iyyar ya shaida wa manema labarai.

Shugaban kwamitin tantance ‘yan takaran, Aminu Masari, ne ya bayyana hakan cikin wata tattaunawa da ya yi da manema labarai a Abuja, ranar Lahadi.

Masari, ya ce, sama da mutane 170 ne suka sayi takardun cikewa domin neman tsayawa takaran mukaman.

Babban taron Jam’iyyar na APC wanda aka shirya gudanar da shi ranar 23 ga watan Yuni, Jam’iyyar ta ce tana nan a kan yanda ta tsara dukkanin mukaman nata shiyya-shiyya, domin kange wasu ‘yan takaran daga shiga zaben da ba shi ne aka kebe wa shiyyan nasu ba.

Fara tantance ‘yan takaran a ranar Lahadi, mun karbi takardun akalla mutane 179, Masari, ya yi alkawarin kwamitin na shi zai tsayu ne a kan ka’idojin da Jam’iyyar ta tanadar na taron.

“Jimillan ‘yan takaran da suka cike takardun su a duk kasarnan, shi ne 179, duk da dai a yanzun ba zan iya tabbatar maku ma da iyakan nasu ba,” in ji shi.

“Mutum zai iya tsayawa takara ne kadai a mukamin da aka kebe wa shiyyan da ya fito. Ya zuwa yanzun dai, duk wadanda suke neman mukaman da aka kebe wa shiyyar Arewa maso yamma, duk daga shiyyar suka fito, ba wani da ya fito daga shiyyar Arewa maso gabas da ya nu na bukatarsa na tsaya a wannan mukamin.”

Tun da farko sai da, Gwamnan Jihar Kaduna, Nasir el-Rufa’i, ya kaddamar da shalkwatar kamfen ta Adams Oshiomhole, wacce ke titin, Aso Dribe, Abuja. Daga bisani, Mista Oshiomhole, ya shaida wa manema labarai cewa, an yi ginin ne domin samar da wajen taro ga magoya baya domin su rika tattaunawa.

Ya kuma bayyana cewa, ya yanke shawarar tsayawa takarar mukamin ne domin saita Jam’iyyar da sake mata fasali.

Ya kara da cewa, ba ya tsoro ko shakkan mutanan da ke son tsayawa takarar a tare da shi, domin manufarsa ita ce a tafi tare da kowa.

“Shigan su takarar zai kara kawata taron ne, Ni ina aiki ne tare da kowa, Allah ne Ya kimtsa mani kaunar na tsaya takarar Shugabancin Jam’iyyar, inda ya yi amfani da wasu shugabannin Jam’iyyar namu, so muke mu rika tafiya tare da kowa,” inji shi.
Advertisement

labarai

%d bloggers like this: