Connect with us

Fadakarwa

Babbar Inuwa

Published

on

08054137080, bilkisuyusuf64@gmail.com

Jama’a Assalamu Alaikum. Barkanmu da haduwa a wannan sabon fili mai suna Babbar Inuwa. Babbar Inuwa fili ne da a ka tanada, wanda zan rika tattaunawa a kan matsaloli da su ke tattare da al’ummmarmu kuma su ke ci ma na tuwo a karya. Zamantakewarmu a yau ta shiga wani rudani da kowa ke zargin kowa, a na yin irin rayuwar nan da Bahushe ke wassafa laifi da ita wato ‘laifi tudu ne, sai ka taka naka ka ke ganin na dan uwanka’ ko kuma a kira shi da ‘gwano ba ya jin warin jikinsa sai na dan’uwansa’.
A irin wannan neman laifin ne jinsina guda biyu (mata da maza) kowa ke ta fafutukar neman ’yanci, wanda a garin neman wannan ’yancin sai kuma a ka fada wani abu daban.
Al’umma ta na kafuwa da kyakkyawar zamantakewa; zamantakewar nan kuwa ba ta inganta sai da muhimman abubuwa kamar haka:

Shugabanci:
Shugabanci ya na farawa ne daga gida. Maigida shi ne da alhakin daukar nauyi kama daga ci da sha da tarbiyya da sauran duk tsarabe-tsarabe da nauye nauyen gida. Shi ne jagora a gunsa a ke sa ran samun dukkan tallafi ga iyali. Wannan shafi zai kalli matsayin maigida da hanyar da ake bi don samun irin maigidan da ya kamata. Sau tari maigida kan shiga tsaka mai wuya kan shawo wasu muhimman matsaloli na iyali musamman yayin kara aure ko ta sanadiyyar kishi daga wajen iyali ko zargi daga taso a bangaren miji ko mata ta sanadiyyar wata kofa da dayansu ya bari. Ire-iren wannan matsaloli da kan taso tsakanin ma’aurata musamman a bangaren shugabancin maigida na gazawa ko na shiga rudani yana daga cikin abubuwan da wannan fili zai tattauna a kai daki-daki tare da kawo mafita dai-dai gwargwado tare da duba a tsanake, don samun ingantacciyar al’umma.

Iyaye Mata:
A bangaren iyaye mata nan ma filin zai zagaya ya ga ma wacce macece ta cancanta da ta zama uwa? Sau tari rawar da wasu iyaye mata kan taka wajen tarbiyyar iyalinsu shi ke nuna lallai a kasancewarsu uwa akwai rauni kwarai da gaske. Za mu duba mai ya kawo raunin? Idan mun samu bakin zaren ta hanyar bincike da nazari za mu kawo yadda mace ke zama zinariya a cikin gidanta. Babu matar da namiji ke aurowa ta zama bora sai idan har ita ta so hakan. Mata da dama su na sa danban zama bora tun daga ranar farko wasu kuma lokacin da suka fara tara zuriya mace marar sa’a ita ke yarda ta zama bora a lokacin da mijinta ya kudurci karin aure ko kuma a lokacin da ta fuskanci wasu matan a waje na jan ra’ayinsa. Mata a gida na da rawar takawa kwarai da gaske kai ! mata fa su ne ruhin gida maigida da yara duk na karkashin kulawarta da kaunarta duk lokacin da mace ta rasa wannan ruhin a gidanta to wannan gidan na cikin barazanar rasa kowanne irin jin dadi da nutsuwa.

Tarbiyya:
Akwai matakan tarbiyya da daman gaske a cikin al’adunmu da zamantakewarmu da ma addininmu. Babu wata al’umma da za ta ci gaba in har ba ta da tarbiyya. Tarbiyyar al’umma ta fi gaban bangare guda kowa na wannan al’umma wajibinsa ne ya sa hannu a cikin al’amuran tarbiyya. Wannan fili zai kawo matakan samun tarbiyya da yadda iyaye ya kamata su tarbiyyantar da ‘ya’yayensu da wasu muhimman jigogi da aka bari ko aka kawar da kai imma a na sane ko kuma a cikin rashin sani wanda sune ginshiki na tarbiyya. Idan a ka yi rashin sa’a aka samu yaro da ke da matsalar tarbiyya me ya kamata iyaye su yi? Duk za a ji a wannan fili na Babbar inuwa da izinin Allah.

Matasa:
Matasa su ne kashin bayin Al’umma sune manyan gobe kuma su ne shugabannin gobe bi hasali ma makomar al’umma a gobe tana hannunsu. Matsaloli in suka mamaye matasa kamar lalaci da rashin aikin yi da shaye-shaye da jagaliya da bauta da shiga rudani da yawon Allah ya ba ku mu samu to fa wannan al’umma ta shiga tsaka mai wuya ta shiga rudani. Fafutikar dawo da wannan da cusawa matasa akidar tashi mu farka tana nan tafe a wannan shafin da yardar Allah.

Cuta Da Magani:
Akwai larurori da daman gaske da ke addabar iyali wanda da damansu suna taka muhimmiyar rawa wajen susuta zamantakewa tsakanin ma’aurata. Wannan shafi zai ke kawo ire-iren wadannan matsaloli da yadda suke shafar iyali kai tsaye.Matsaloli irin su basur da sanyi da dattin na ciki da na mara da sauran matsaloli na bangaren maza duk wannan fili zai kawo su daki-daki da hanyar da za a bi don magance su. Ko a bangaren mata akwai ire-iren wadannan matsaloli da suke zama ummul’aba’isin gigita zamantakewar iyali. Wannan filin zai kawo matsalolin mata da suka shafi bangaren lafiya musamman wanda ke kawo cikas a auratayya kamar rashin gamsuwa yayin mu’amalar aure da rashin ni’ima da bushewa da cutocin sanyi da sauran larurori wannan shafin zai tattauna a kansu kuma ya tanadi magani ingantacce don samar da waraka da yardar Allah. Akwai cutoci da dama kamar su Ulcer da Hawan jini da cutoci wanda wannan fili zai ke kawowa tare da kawo hanyoyin da ya kamata a samu waraka. Hatta yara akwai tanadinsu don samar da yara masu hazaka da fikira a wannan fili na babbar inuwa.

Jin kai Da Taimakon Juna:
A zamantakewarmu akwai mai karfi da raunanne wanda wajibine a tsakaninsu su taimaki juna. dan’adam kowanne yana da irin nasa amfanin da yake yi wa dan’uwansa. Mata masu rauni kamar zawarawa wadanda mazajensu suka rasu ko aurensu ya mutu da ‘yanmata musamman wadanda suka sami jinkirin aure dukkansu suna bukatar taimako don suna fuskantar matsaloli na musamman wanda wannan fili zai kawo irin matsalolin da suke fuskanta da irin taimakon da suke bukata kama daga shawarwari ko jan hankali ko kuma jan kunne.

Jagogorin Al’umma Da Wadanda A Ke Jagoranta:
Wannan fili zai kalli shugabannin al’umma ‘yan siyasa da ma wadanda ke tallafe da wasu madafun iko da yadda ake samun takun saka da rashin yarda da amana a tsakani da rashin kauna da jin kai wanda kowa yana da nasa laifin amma ya taka yake laluban na dan’uwansa. Wannan fili zai yi bincike ya kawo nazarinsa tare da warware zare da abawa da neman mafita.

Wannan fili, fili ne na tattaunawa tsakanina da ku al’umma, don samun bakin zaren me ke damun al’ummarmu da ta yaya za a sami waraka ko daidaito. Zan yi maraba da tambaya ko neman karin haske ko ma neman warware wata matsala da ta addabe ku ta bayar da shawara ko tura ku zuwa inda ya dace.
Allah ya yi ma na jagora, ya zaunar da al’ummarmu lafiya da kwanciyar hankali da warakar matsalolinmu na lafiya zahiri da badini, amin.
Advertisement

labarai

%d bloggers like this: