Rundunar ‘yansandan Jihar Nasarawa ta ƙaryata rahotannin da ke cewa ‘yan bindiga sun sace ɗaliban makarantar St. Peter’s Academy, Rukubi, da ke Ƙaramar Hukumar Doma.
Sun ce labaran da ke yawo a yanar gizo ba gaskiya bane.
- Firaministan Sin Ya Ce A Shirye Yake Ya Yi Aiki Da Zambiya Da Tanzaniya Wajen Gina Sabuwar Cibiyar Tattalin Arziki
- NDLEA Ta Cafke Mutane 230 Da Miyagun Ƙwayoyi A Kano
‘Yansanda sun bayyana cewa wasu ɗalibai ne suka ga mafarauta ɗauke da bindigogi a kusa da makarantar shi ne suka tsorata.
Wannan ne ya haifar da jita-jitar sace ɗalibai a kafafen sada zumunta.
“Rahoton ƙarya ne kuma babu wani abu da ya nuna an sace ɗalibai” in ji SP Ramhan Nansel, jami’in hulɗa da jama’a na rundunar.
‘Yansanda sun tura jami’ai da sojoji zuwa makarantar, amma suka gano babu ɗalibai da aka sace.
Shugaban makarantar ya kuma tabbatar da cewa rahoton da ke yawo ba gaskiya ba ne.
Hukumomi na ci gaba da lura da yankin don tabbatar da tsaro.
An roƙi jama’a da ‘yan jarida da suke tabbatar da gaskiyar labari kafin su wallafa su.














