Connect with us

LABARAI

Babu Abin Da Ministocin Buhari Ke Yi Sai Facaka – Sule Lamido

Published

on

Tsohon Gwamnan Jihar Jigawa kuma dan takarar neman tsayawa takarar Shugabancin kasa a shekarar 2019, Alhaji Sule Lamido, ne ya bayyana hakan gaban dubban Jama’a a garin Lafia Jihar Nasarawa.

Lamido ya ce, Jam’iyyar APC mai Mulki ta zama matattaran masu laifuka. Ya ce, Jam’iyyar APC ta ce duk wadanda suka yi Mulki a baya barayi ne, kuma za ta kama su, amma da zarar mutum ya sace dukiyan al’umman Jihar shi, sai ya sauya sheka daga wata Jam’iyya zuwa APC sai ya zama mutumin kirki.

Lamido ya bayyana haka ne lokacin da ya je yakin neman zabe, a garin Lafiya, Jihar Nasarawa. Ya ce, Gwamnatin da ke Mulki ta maida EFCC karen farauta, tana mata farautar barayi.
Ya ce, da EFCC ake yiwa mutum barazana a bayyana masa abin da ya sata a kuma ce da shi ko ya dawo APC ko a kama shi.
Ya ce, an yi haka da Uzo Kalu,  sannan an yi wa Tsohon Gwamnan Akwa Ibom. Lamido ya ce, an yi wa tsohon Gwamnan barazanan haka, ya bi Buhari zuwa London, Buhari ya tabbatar masa cewa idan ya dawo APC babu abin da zai faru da shi.

Ya kara da cewa, akwai ire-iren su da yawa wadanda suka yi mulki kuma suka sace dukiyar Jihar, wasu ma babu aikin kirki da suka yi a Jihar su, amma yanzu su mutanen kirki ne saboda suna APC.

Sule Lamido ya ce, “a shekarar 2015 idan wani ya ce, sai Buhari, idan ka ce da shi a yi addu’a, Allah Ya zaba mana ma fi alheri, sai a ce da kai ‘arne’, dan kudu. Amma yanzu da Buhari yake mulki al’umma suna ji a jikinsu, da dama suna danasani”.

Saboda babu ayyukan alheri da Gwamnatin Buhari ta kawo, sai dai kara barnata dukiyar kasa. Ya ce, Buhari ya yi alkawura da yawa kafin a zabe shi, cikin su har da abubuwa uku da aka ce zai samar da su.
Tsaro – Tattalin arziki – Yaki da cin hanci da rashawa. Amma yanzu wane ne ya samu?

Kasar babu tsaro ko kadan, har ma gara Gwamnatin baya. Yanzu kashe-kashe ya yawaita, idan ka je Maiduguri, kullun kisan al’umma ake yi, ga Zamfara ga Benuwe ga Nasarawa ga Taraba ga Adamawa ga Neja. Ya kara da cewa, yanzu saboda lalacewa da rashin sanin hakkin ‘yan kasa. Mutum bai isa ya bi wasu hanyoyi a kasan nan ba sai ya gamu da masu sace mutane. Ya ce, hatta hanyar Abuja zuwa Kaduna babban abin kunya  sace mutane ake yi babu dare babu rana.

Ya kara da batun yadda tattalin arzikin kasa ya lalace, al’umman kasa suka shiga cikin wahala, talauci, yanwa, da  tsadan rayuwa. Gwamnatin Buhari cin hanci da rashawa ya mamaye ta, babu abin da Ministoci ke yi sai facaka.

Da yake zantawa da Wakilin Leadership A Yau Juma’a, bayan kammala taron. Da aka tambaye shi makasudin tsayawar shi takara. Ya ce, “Saboda ni dan Nijeriya ne, ina da daman tsayawa takara kamar yadda tsarin mulki ya ba ni dama haka ya ba kowa dama.
Duk dan kasa yana da ‘yancin yin takara saboda ya ba da gudumawarsa.

Da yake amsa tambayar ko zai iya kwatanta wannan Gwamnatin ta APC da ta PDP, sai ya ce, a tambayi Jama’a saboda yanzu kowa na gani yana kuma ji a jikinsa ko a rigar sawa kawai da abinci da kwanciyar hankali yanzu al’umman kasa ne za su ba da labara, ya ya bambancin yake.
Advertisement

labarai

%d bloggers like this: