Daga Rabiu Ali Indabawa
Ga dukkan alamu babu wata alama da ke nuna sasanci tsakanin Ƙasashen Saudiya da Ƙatar. Sarkin Kuwait Sheikh Sabah al-Ahmad Al-Sabah wanda ke shiga tsakani kan rikicin ƙasashen Saudiya da Ƙatar ya ce har yanzu babu alamun kawo ƙarshen rikicin, ganin yadda ɓangarorin biyu ke nuna halin ko in kula akan sabanin da ke tsakaninsu.
A jawabi da ya gabatar ga Majalisar ƙasar a yau, Sheikh Al Sabah ya bayyana fargaba kan yadda har yanzu aka gaza magance rikicin, wanda ya shiga watanni 5 da farawa, yana mai cewa babban muradinsa a yanzu bai wuce ganin an ceto ƙungiyar ƙasashen Yankin Tekun Fasha da ke neman durƙushewa ba.
Ko a ziyarar da Sakataren harkokin Amurka Reɗ Tillerson ya kai wasu daga cikin ƙasashen yankin Gulf cikin ƙarshen makon da ya gabata, ya shaida cewa Saudi Arabiya ba ta shirya kawo ƙarshen rikicin da ke tsakaninta da Ƙatar ba.
Sheikh Al Sabah ya ce za su ci gaba da bin matakan lalama don ganin an samu fahimtar juna tsakanin ƙasashen biyu.