A ci gaba da mayar da zazafan martani da jarumin Kannywood Adam Zango yake yi, ya kuma bayyana cewar akwai tarin mayaudara da mahassada a masana’antar Kannywood.
Zango, ya bayyana haka ne a wani faifan bidiyo da aka wallafa a Facebook, inda yake bayyana yadda da yawa daga cikin abokan sana’arsa suke fatan ganin ya daina fitowa a cikin shirin fim.
- Kalau Nake Babu Abin Da Ke Damun Kwakwalwata – Adam Zango
- Ra’ayoyin Kasashen Duniya Game Da Harin Da Iran Ta Kaddamar A Kan Isra’ila
“Duk da cewar akwai da yawa daga cikinmu a masana’antar wadanda suke da halaye nagari amma wadanda suke da halin mugunta da hassada sun fi yawa,” in ji Zango.
“Saboda haka nan bada jimawa ba mai yiwuwa ne a nemeni a rasa a Kannywood domin kuwa zan koma wata sana’a wadda ba fim ba saboda na zauna lafiya kalau tare da iyalina da kuma ‘yan uwa da abokan arziki,” in ji shi.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp