Babu Wata Kabila Da Take Sama Da Wata A Kasar Nan ― Gbajabiamila

Wakilai

Daga Yusuf Shu’aibu,

Shugaban majalisar wakilai, Femi Gbajabiamila ya yi gargadin cewa,
babu wata kabila  a cikin kasar nan da take sama da sauran kabilu, sai
dai ana a martaba juna domin samun lafiya da kwanciyar hankali.

Shugaban majalisar ya bayyana hakan ne jim kadan bayan fitowa taro
tare da shugaban kasa, Muhammadu Buhari a fadarsa da ke Abuja. Ya
bayyana cewa, akwai bukatar tattaunawa a tsakanin ‘yan Nijeriya. Ya
tabbatar da cewa lokacin da majalisa ta dawo bakin aiki daga hutunta,
za ta ci gaba da tattauna wajen samo masalaha.

Da yake magabana a kan rikicin da ke faruwa a yankunan Kodu-Maso-
Yammaci da Kudu-Maso-Gashi na Fulani makiyaya, ya ce, “ya kamata a
tattauna da dukkan bangarorin domin samo hanyoyin magance rikicin.

“Bana tunanin akwai kabilar da take sama da wata kabila a Nijeriya.
Kabilar da ke Kudu-Maso- Yammaci ba ta fi kabilar Arewaci ba, haka
kuma kabilar Arewaci ba ta fi na yankin Kudanci ba. Ya kamata mu
martaba kasuwancinmu da yankunanmu da kabilunmu fiye da duk wani abun
da zai janyo tashin hankali.

“Abin da ya fi dacewa shi ne, mu zauna tare domin mu tattauna domin
sawo bakin zaran. Yana tunanin kowa zai iya hakan. Za a fara daukan
wannan mataki tun daga majalisa.

“Ina sa ran za mu dawo aiki a ranar Talata mai zuwa, na tabbata za a
tafka muharawa a zauran majalisa dangane da lamarin, sannan majalisa
za ta samar da hanyoyin samun masalaha wanda zai dace a ra’ayin ‘yan
kasa.”

A kan abubuwan da suka tattauna da shugaban kasa Buhari kuwa, shugaban
majalisan ya bayyana cewa sun gaba da shugaban kasa ne a kan wasu
abubuwa da suka shafi kasar nan.

Bisa sabun da katin mamban jam’iyyar APC, Gbajabiamila ya bukaci
dukkan mambobin jam’iyyar da su yi kokarin sabunta katukansu na
jam’iyya.

“Ina kira ga mambobin jam’iyyar APC, wadanda ba su da katin jam’iyya
da su yi amfani da wannan dama su yi kamar yadda shugaban kasa ya
sabunta na shi.

“Saboda babban zaban shekarar 2023, zai kasance za a iya daukan kowani
mutum ya wakilce jam’iyya a lokacin zaben.

“Kar a manta yin rijista shi ne babban dalili da zai bayar da damar
zabe na cikin gida har zuwa zabe n agama-gari. Ya kamata kwani dan
jam’iyya ya kasance yana da katinsa kamar yadda muka dade muna kira ga
mutane su yi,” in ji shi.

Exit mobile version