Wata Kotun Tarayya da ke Abuja ta bayar da belin, Sanata Rochas Okorocha, kan naira miliyan 500 bayan gabatar da mutum daya da zai tsaya masa.
Jaridar Punch ta rawaito Alkalin Kotun, Inyang Ekwo na cewa bada belin zabi ne na kotu, kuma an dage sauraron shari’ar zuwa watan Nuwamba.
Okorocha Ya Musanta Zargin Damfarar N2.9bn, Zai Ci Gaba Da Zama A Hannun EFCC
Sannan a cewar jaridar, alkali Ekwo ya ce wanda zai tsayawa Okorocha a belin dole ya kasance ya na da kadarori a inda ake zaman kotun, kuma dole ya bada jinginar takardun filin nasa.
Sannan alkalin ya bukaci sanatan ya bada fasfo dinsa na tafiya, a kuma sanar da hukumar shige da fice matsayar kotun.
Ya kuma umarci ka da Sanata Rochas ya kuskura ya bar kasar ba tare da izinin kotu ba.
Bada belin tsohon gwamnan da EFCC ta kama kan badakalar naira biliyan 2.9 a lokacin da ya ke kujerar gwamnan, na zuwa ne a rana ta biyu na tantace masu neman takara a inuwar jam’iyyar APC mai mulki.
Tsohon Gwamnan na Imo kuma ɗan Majalisar Dattawa, Sanata Rochas Okorocha, mai shekara 59, na daga cikin masu neman takarar shugaban ƙasa a APC.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp