Gwamna Abubakar Atiku Bagudu na Jihar Kebbi, ya gabatar da takardun shaida a gaban kotun sauraron kararrakin zabe da ke zamanta a Birnin Kebbi, inda ya ke kalubalantar nasarar lashe zaben Sanata Muhammadu Adamu Aliero, PDP da INEC a gaban kotun ta hanyar lauyansa.
Idan za a tuna dai Bagudu yana kalubalantar nasarar da Sanata Aliero ya samu kan zaben Sanatan Kebbi ta tsakiya da ya gudana a kwanakin baya.
- Nijeriya Za Ta Yi Kawance Da WHO Kan Rigakafi
- Gwamnatin Kebbi Za Ta Hada Hannu Da Masanan Masar Wajen Bunkasa Noma Da Kiwo
Ci gaba da gabatar da takardun wani bangare ne na zaman sauraren karar na matakin farko na sauraren karar da ya shigar da kuma neman kotu ta karbe su a matsayar shaida kamar yadda dokar zabe ta tanada.
Lauyan Gwamna Bagudu, Barista Lagalo D. Lagalo, ya ce, “A karamar hukumar Kalgo mun nemi gabatar da fom 32 na EC8A1, amma 30 ne kawai a wurinsu biyu ba su samu ba, sun gabatar da fom guda 8 na EC 8C1. Ya kuma mika fom din EC8C1 na kananan hukumomi guda takwas wadanda su ne suka hada gundumar Kebbi ta tsakiya ta jihar a matsayin wani bangare na takardun shakda ga abin da yake kalubalantar ga zaben na Sanata Muhammadu Adamu Aliero.”
Haka kuma ya gabatar da fom daya na takardar takaitaccen sakamako na EC8B1 watau (summary results sheet) da kuma nau’i daya na EC8E1 bayyana sakamakon zabe. Daga nan sai ya sanar da kotun cewa, “Duk takardun da aka jera a shafi na 28,29, 30,31 da 34 ba su samuwa, amma za a gabatar da su a ranar da za a dawo zaman na gaba,” in ji shi”.
“Duk da haka, har yanzu a karamar hukumar Kalgo mun lissafta fom biyu EC40G (pu) amma daya ne kawai ake samu a mazaba ta uku a runfa ta daya. Ya bayyana wa kotun cewa a zaman na yau abin da suke da shi ke nan. Amma a ranar da aka sanya don dawowa zaman Kotun na gaba za a gabatar da duk takardun da aka bayyana cewa babusu a hannu za a tabbatar da cewa an gabatar da su a gaban kotun.”
Kazalika, Barista Lagalo ya tabbatar wa kotun za a shigar da takardun a ranar da za a dawo zaman Kotun daga bisani kuma ya nemi a dage zaman har zuwa ranar Litinin 15 ga watan Mayu na shekara ta 2023 don kammala gabatar da shedar takardu.
A bangarensu Lauyan sanata Adamu Aliero, Barrister Aminu Hassan a matsayin wadanda ake kara na farko, lauyan PDP a matsayar wadanda ake kara na biyu D.D Dodo SAN wanda lauyan hukumar INEC da ake kara na uku Barrister Magnus Ihejirika ya tsayawa yayin gabatar da shaidar takardun a gabn kotun sun amince da dage cigaba da Shari’ar zuwa ranar Litinin 15 ga watan da muke ciki.
Kotun ta amince da takaddun da aka gabatar a gabanta kuma an yi musu alama azaman Nunin AAB1 zuwa AAB 16, AAB17G, AAB 19 da AAB 20 bi da bi.
Shugabar kotun, Honourable Justice Margret Opara ta ce, “Bisa yarjejeniyar da lauyoyin na dukkan bangarori suka amince an dage sauraren karar zuwa ranar Litinin 15 ga Mayu 2023 don ci gaba da zaman sauraron karar.