A kokarin da gwamnatin shugaban kasa Muhammadu Buhari ta mayar da hankali wajen bunkasa bangaren gas domin farfado da tattalin arziki da samar da ayyukan yi ga miliyoyin ‘yan kasa wajen tsamo su daga kangin talauci. bangaren gas a Nijeriya a yanzu haka yana ci gaba da bunkasa wanda yake gogayya da man fetur wajen samar da kudaden shiga a Nijeriya. Shugaban hukumar kamfanin (NNPC), Mista Mele Kele Kyari shi ya bayyana hakan wajen taron makamashi na duniya. A cewarsa, a yanzu haka a Nijeriya bangaren gas yana bai wa kasar nan damar tanadar dala biliyan uku zuwa biliyan hudu wanda ake amfani da shin a cikin gida da na kasashen ketare.
Kyari ya kara da cewa, bisa bayanan da masana makamashi suke gabatarwa a kowani lokaci, Nijeriya ta kasa ce wacce take da dimbin man fetur da kuma gas, wanda a yanzu haka ta sami shiga cikin kasashe guda 10 da ke da karfin gas a duniya. Shugaban NNPC ya ce, bangaren gas ya samar da karfin wutar lantarki wanda ya kai kashi 60 a cikin kasar nan. Ya kara cewa, a yanzu bangaren makamashi ya rage yawan marasa ayyukan yi wanda da a baya suke fama da matsananci talauci, amma sakamakon bunkasan bangaren ya sa an samu mutane masu dinbin yawa da suka sami ayyukan yi wanda sukee kulawa da kansu.
“Akwai dinbin hanyoyin zuba jari a bangaren makamashinmu, musamman ma a bangaren gas wanda muke samun sama da dala biliyan 10. Haka kuma akwai wasu ayyuka wanda za a iya samun biliyan uku zuwa biliyan biyar idan aka samu nasarar zuba jari a wannan bangar na gas,” in ji Kyari.
Ya cigaba da cewa, a yanzu haka an mayar da hankali a bangaren gas saboda samun kudaden shiga a cikin kasar nan, wanda ake iya samun kasa tsakanin 250,000 zuwa 350,000 a duk kullum wanda yake kokarin cike gurbin da ake samu a baya. Kyari ya ce, gas a Nijeriya yana da matukar mahimmanci wanda a yanzu ake ta samar da sauyi a bangaren mai da kasar nan take fitarwa a kasashen ketare. Ya ce, bangaren gas a Nijeriya a yanzu haka ya karu matuka tun daga wanda ake amfani da shi a cikin gida har zuwa wanda ake fitarwa kasashen. A cewarsa, kasar nan ta samu karuwar gas a cikin burane wanda a yanzu haka ake shirin fadada bangaren gas zuwa yankunan karkara.
Ya ce, “an bayyana cewa nan da shekaru 30 za a dunga hako mai ganga miliyan 100 a duk kullum domin yin amfani da shi a cikin gida.
“Domin haka, man fetur da gas za su ci gaba da bunkasa a nan gaba, domin kasuwancinsu gaskiya ne. kowacce kasar da ke da arzikin man fetur da gas tana kokari ta fara wadatar da ‘yan kasarta tukunna ta fitar da shi zuwa kasashen ketare, wannan shi ne muke kokarin gudanarwa a Nijeriya a yanzu haka.
“Muna fuskantar gagarumar nasara a bangaren gas wanda cikin dan karamin lokaci mun samu kudade masu yawa a bangaren ghas. Lallai a yanzu haka muna ci gaba da ganin alfanun gas a Nijeriya,” in ji shi.
Shugaban kamfaninn NNPC ya ce, Nijeriya tana kokarin farfadowa daga bangaren mai sakamakon matsalolin da aka samu na raguwar fara shin danyan mai a kasuwan duniya wacce cutar Korona ta haddasa a watannin baya. Ya ce, a yanzu haka Nijeriya tana samun haraji mai yawan gaske.
A nasa bangaren, tsohon shugaban NNPC Barkindo ya ce, “idan ana ci gaba da bunkasa makamashi a Nijeriya za a samu gagaruman kudaden shiga a wannan bangare.
“bangaren makamashi shi yake tabbatar da samuwar ingantacce wutar lantarki a cikin kasa, domin da shi ne ake samar da wutar lantarki mara lissafuwa a ko’ina a fadin duniya.
“Cig aba da samun karancin gas zai iya hana mu samun ingantacciyar wutar lantarki a Nijeriya.
“Idan muka duba matsalolin da muke fuskanta a bangaren wutar lantarki, akwai bukatar mu bunkasa bangaren gas domin samun wutar lantarki mai daurewa a Nijeriya,” inji shi.