Bankin Duniya ya yi gargadin cewa, ya zama wajbi a gaggauta daukar matakan gaggawa, domin a kawar da talauci a tsakanin kasashe 23, nan da 2025.
A cewar wadannan kasashen sun kasance suna da alumar da yawan su ya kai kimanin kashi 40, wadanda kuma suna dogara ne a kan kasa da Dala 2.15
- Bai Kamata Kungiyar EU Ta Biyewa Masu Burin Rusha Alakarta Da Sin Ba
- Da Rancen Naira Tiriliyan 13 Za A Cike Gibin Kasafin Kudin 2025 — Edun
Kazalika, Bankin ya kara da cewa, wadannan kasashen, dimbin bashi, ya dabai bayesu, tare da rashin samu tallafai, daga kasasehn duniya.
Bankin ya jaddada cewa, ya zama wajbi kasashe masu tasowa, su tabbatar da suna habaka tsarin sun a tara haraji, tsarin kashe kudade da kuma samo taimakon daga kasashen duniya, domin su kasance masu samar da ci gaba a kasashen su.
A cewar Bankin idan ba su samo masu zuba hannun jari tare da daukin kasashen duniya ba, rayuwar wadannan alumomin na wadannan kasashen, za su gaba da zama a cikin talauci.
Daya daga cikin binciken rahoto da ake dako na makokar tattalin arzikin duniya wanda za a fitar a ranar 14 ga na 2025, ya nuna cewa, daga cikin kasashe 39, kamar su; Indiya, Indonesia da kuma Bangladesh, tun a 2000 suka daga matsayin ‘yan kasarsu da samun kudaden shiga ‘yan kadan wanda hakan ya nuna cewa, sauran kasashe, sun kasance ba su da karfin tattalin arziki.
Sama da shekaru 15, wadannan kasashen sun samu nasarar tsallake siradin tsadar ruwa, wanda hakan ya sanuya tattalin arzikinsu ya karu.
Idan har ba a samar da wasu manyan sauye-sauyen a tsakanin wadannan kasashen masu tasowa ba, daga cikinsu, shida ne kacal za su samu damar daga matsayin alumomin su marasa karafi a 2050.
Kazalika, aukuwar tashe-tashen hunkula, sauyin yanayi da tabarwar tattalin arziki, za su iya mayar da wadannan kasashen baya.
Babban mai fashin baki a Bankin na Duniya kuma Mataimakin Shugaba a bangaren bunkasa tattalin arziki Indermit Gill, ya sanar da cewa, shekaru 25 masu zuwa, za ta kasance wata dama ga wannan kasashen masu tasuwa.
Bugu da kari, wadannan kasashen sun kasance suna dimbin albarkatun kasa
Shi ma wani kwararre a Bankin na Duniya Ayhan Kose, ya jaddada mahimmancin lalubo da mafita a kan wadannan kalubalen da kasashen ke fuskanata, musaman domin a kawo karashen talauci.