Bankin Duniya ya kudiri sake dawo da Kadada sama da milyan daya ta kasar noma, wanda Hamada ta yi wa kutse aka kuma yi watsi da sakamakon ayyukan haramtattun masu hakar ma’adanan wannan kasa a Arewacin Nijeriya.
“Bisa goyon bayan Gwamnatin Tarayya tare da gwamnoni 19 da ke jihohon Arewacin Nijeriya, wannan kasar noma da tuni aka yi watsi da ita, za a iya sake dawo da ita domin ci gaba da yin noma a cikin shekaru shida kacal, musamman don kara habaka ayyukan noma a jihohin da ke yankin Arewa”, a cewar Babban Bankin.
Wani babban jami’in aikin kula da yanayin aikin noma da samar da ingantacciyar kasar noma (ACReSAL), Abdulhameed Umar ya tabbatar da hakan a yayin da ke nasa jawabin a taron bita na kwanaki biyu da aka shirya wa wasu daga cikin jami’an aikin na ACReSAL da ke a jihohi 19 na Arewacin wannan kasa.
Taron, wanda ya gudana a garin Jos da ke Jihar Filato, Umar ya kara da cewa, kasar noma a Arewacin Nijeiya na ci gaba da fuskantar kwaranyowar Hamada, gurbatar muhalli, zaizayar kasa da kuma hakar ma’adanan kasa, musamman a Jihohin Nasarawa, Zamfara da sauran makamantansu, wanda hakan ke tilasta manoma da makiya a yankunan yin hijira zuwa wasu yankunan kasar daban.
Har ila yau a nasa jawabin, Jami’in hukumar ACReSAL na Jihar Filato Garuba Gowon ya bayana cewa, manufar aikin shi ne domin jawo hankalin jihohin da ke kasar nan kan afkuwar dumamar yanayi da kuma kokarin da ake yi wajen samar da wadataccen abinci mai gina jikin dan Adam.