Connect with us

RIGAR 'YANCI

Bankin Keystone Ya Bai Wa Gwamnatin Gombe Tallafin Kayyakin Yaki Da Korona

Published

on

Bankin Keystone ya bi sahun bangarori da kungiyoyi na tallafa wa kokarin gwamnatin Gombe na ci gaba da yaki da cutar Korona, inda bankin ya bada tallafin kayyakin aiki domin ci gaba da fatattakar annobar.
Wakazalika, shi ma Manajan Bankin GT a jihar Gombe Hamza Yuguda ya bada tasa tallafin domin yaki da cutar Korona a Gombe.
Manajan Bankin Keystone PLC a jihar Gombe, Mista Liyo Mohammed shine ya jagoranci mika tallafin a madadin hukumar gudanarwa na bankin a jiya, inda ya shaida cewar sun dauki matakin kawo tallafin ne domin agaza wa kokarin gwamnatin jihar na yaki da cutar Korona.
Kayyakin da bankin ya bada tallafi wa Gombe sun hada da gadajen kula da lafiya da suke kunshe da dukkanin kayansu guda 5, katifu da daman gaske, sinadarin wanke hannu guda 300 masu nauyin 100ml, fakej-fakej na abin rufe hanci da baki guda 60, fakej-fakej na safar hannu guda 60.
Mista Mohammed ya kara da cewa, tallafin na karkashin shirin bankin na sauke nauyin taimaka wa al’umma ne, inda ya ke mai karawa da cewa bankin ya nemi taimaka wa gwamnatin ne a irin wannan lokacin da ake kan yaki da cutar Korona.
A cikin kwafin sanarwar manema labaru da Kakakin gwamnan Gombe Ismaila Uba Misili ya fitar, ya shaida cewar kwamitin yaki da cutar Korona a jihar ya kuma amshi tallafin na’urar daidaita numfashi guda biyu wato ‘Osijin concentrators’ daga hannun Hamza Yuguda, Manajan bankin Guarantee Trust Bank, GTB a jihar Gombe, inda ya taimaka wa kokarin gwamnatin jihar na yaki da cutar Korona.
Shugaban kwamitin yaki da cutar Korona a jihar Gombe, Farfesa Idris Muhammad ya tabbatar da cewar kayyakin tallafin da suka samu din zai dauki tsawon lokaci yana taimaka wa kokarin gwamnatin jihar na yaki da cutar, sai ya nuna godiyarsu wa bankin Keystone da kuma Manajan GT bank Hamza Yuguda a bisa wannan tallafin da suka bai wa gwamnatin.
Advertisement

labarai

%d bloggers like this: