Abubakar Abba" />

Bankuna Sun Yi Asarar Kudin Ruwa Na Watanni 18 A Nijeriya

Wakilun mu ya jiyo cewar, Babban Bankun Nijeriya CBN, ya bukaci bankunan su manta da cajin kudin ruwa akan rarar man fetur nayan kasuwa masu sawo man daga Yunin 2017 zuwa Disambar 2018. CBN ance ya turawa bankunan sakon ne a wani taro da ya yi dasu a Disambar 2018, inda hakan yana daya daga cijin kokarin da akeyi na kawo karshen rikicin bashin na kudin rarar man da masu shigo da man suke bin gwamnatin tarayayyar. Wata majiya mai tushe kusa da yan kasuwar wadda ta tsegumtawa wakilin mu matakin na CBN ta ce, “mun gana a Disamba a Abuja daya ganawar kuma anyi ta ne a Jihar Legas, inda CBN ya shedawa bankunan su ja kudin ruwan baya na Yulin 2017 har zuwa yau. A cikin littattafan ajiya na bankunan, yan kasuwar suna bin gwamnatin tarayya naira biliyan 800, a saboda hakan wannan wata tattaunawa ce da CBN a madadin gwamnatin.” Bankin na CBN ya shedawa bankunan maimakon ayi asarar dukkan kudaden, suja kudin ruwan baya da kashi daya bisa uku mu kuma zamo samo hanyoyin biyan sauran da suka rage. CBN ya yi hakan nea madadin gwamnatin da ake bi bashin. Ya ce, wasu yan kasuwar sun karbi takardar bayanai daga ofishin kula da bashi na kasa DMO wanda zai nuna a a ranar 31 ga Disambar 2019, don biyan kudin farko naira biliyan 236. Babban Sakatare na kungiyr DPPMA na kasa Misat Olufemi Adewole da kuma Kwantirolan ayyuka na kass na IPMAN Mista Mike Osatuyi, duk sun tabbabatawa da wakilin mu maganar hakan. Acewar Adewole, bukatar ta fito ne daga gwamnatin tarayya zuwa ga bankunan, inda Gwamnan CBN ya tsaya a madadin gwamnatin na cewar, dukkan kudin ruwan na bankunan suja kudin ruwan baya akan kudin rara ta mai samfarin PMS da ya daina yin aiki a ranar 30 ga watan Yunin 2017. Da aka tambaye ko daukacin yayan DAPPMAN da suma suke bin bashin na rarar man sun samu takardar bayanan daga na biyan kashi na farko na bashin ya ce,wasu sun samu wasu kuma suna son su kauracewa hukuncin kotu. Sai dai, wasu bankunan sunce suna jiran kudin tsari ne daga CBN kafin su fars yin wsni abu akan takardar, inda hakan ya jefa yan kasuwar a cikin rudani tun loacin da aka mika masu takardun a Dismba. Osatuyi ya ce, babu daya dan kungiyar ta IPMAN da ya karbi ko kwandal da yake bin gwsmnatin tarayyar na naira biliyan biyu. A cikin watan Disambar Babban jami’I na kula da ayyuka na kamfanin NNPC, Mista Henry Ikem-Obih baysn ksmmals gana ds jami’an yan kasuwar a grin Abuja, ya shedawa manema labarai cewar, za’a biya sauran udin na rarar mai da yan kasuwar suka yi ikirari suna bin gwamnatin tarayya a 2019. Acewar ss, mun amince zamu biya kudin bayan an buya na farko yan kasuwsr zasu kafa kwamiti don yin aiki akan bayanan na yadda za’a biya na karo na biyu a 2019 da kuma karshen da zs’a biya a 2020. G wsmnatin ta himmatu matuka wajen wajen son ta biya kudin na farko kamar yadda ta yi alkawari a baya. A karshe Ikem-Obih ya ce, gwamnatin tarayya ta hakikance na buyan kudin ta hanyar yin amfani da takardar wadda daidai take da yin amfani da zallar kudi kuma zata iya durkushewa nan take. Majalisar Dattawa a ranar 31 ga wstan Okutoba, tayi tir da gwsmnatin tarayya akan kin biyan kudin duk da cewar gamaiyyar Majalisar kasa ta amince da biyan tun a wstan Yulin 2018.

Exit mobile version