• English
  • Business News
Saturday, November 1, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Barawon Da Ke Ihun Kama Barawo

by CMG Hausa
3 years ago
Barawo

Sinawa kan bayyana wanda ke neman dora laifinsa a kan wani a matsayin “barawon da ke ihun kama barawo”. Gaskiya kam, ’yan siyasar kasar Amurka ma sun amsa wannan suna. 

Ga shi dai, kwanan nan ba da jimawa ba, Amurka ta sake “ihun kama barawo”, inda cibiyar GEC karkashin ma’aikatar harkokin wajen kasar ta fitar da rahoton da ya zargi gwamnatin kasar Sin da neman shawo kan ra’ayoyin al’umma a game da jihar.

  • Firaministan Pakistan Ya Gode Wa Sin Bisa Taimakon Da Ta Baiwa Kasarsa Wajen Yaki Da Ambaliyar Ruwa

Amma gaskiyar lamari shi ne Amurka da ma sauran kasashen yamma su ne suke gurbata gaskiya da gurgunta fahimtar jama’a a kan abubuwan da ke faruwa a jihar ta Xinjiang, wandanda suka kawar da kai daga ci gaban tattalin arziki da zaman al’umma da aka cimma a jihar da ma yadda al’umma ’yan kabilu daban daban ke zaman walwala a jihar, kuma suka yi amfani da karfinsu ta fannin kafofin yada labarai, suka yada karairayin da suka shafi “kisan gilla” “aikin tilas” da sauransu a jihar Xinjiang, don cimma burinsu na dakile ci gaban kasar Sin bisa “batun Xinjiang”.

“Mun san cewa, babu wata matsala a Xinjiang, amma kirkiro matsalolin hakkin bil Adam na aikin tilas da kisan kare dangi, mataki ne mai amfani, don cimma burinmu na jefa gwamnatin kasar Sin cikin mawuyacin hali”, wannan shi ne furucin da jami’an diplomasiyya na kasar Amurka dake kasar Sin suka yi kwanan baya, lamarin da ya nuna ainihin abin da Amurka ke neman cimmawa.

Yayin da Amurka ke shafa mata bakin fenti, shin bai dace ba kasar Sin ta mayar da martani? Sai dai hakan ya zama “neman shawo kan ra’ayoyin al’umma a game da jihar Xinjiang” kamar yadda rahoton da Amurka ta fitar ya bayyana. Lallai Amurka ta amsa sunan “barawon da ke ihun kama barawo”.

LABARAI MASU NASABA

Xi Jinping Ya Tattauna Da Shugaban Koriya Ta Kudu Lee Jae-myung 

Xi: A Hada Kai Wajen Gina Al’ummar Bai Daya Ta Asiya-Pasifik

Idan ba a manta ba, don neman kaddamar da yaki a Iraki, Amurka ta taba zargin Iraki din da mallakar makaman kare dagi bisa farin garin da ta nuna wanda ba a tabbatar da yanayinsa ba.

Amurka tana yawan satar sauraron bayanan jami’an kasa da kasa, a yayin da kuma take zargin wasu da satar bayanai ta yanar gizo. Sai kuma a watan da ya gabata, kakakin majalisar wakilan kasar Amurka ta kai wata haramtacciyar ziyara yankin Taiwan na kasar Sin duk da rashin amincewar da kasar ta Sin ta nuna da kakkausar murya, daga bisani kuma ta zargi kasar Sin da “mayar da martanin da bai dace ba, wanda ya tsananta yanayin da ake icki a zirin tekun Taiwan.”
Mike Pompeo, tsohon sakataren harkokin wajen kasar Amurka ya taba bayyanawa a fili cewa, “Da karairayi da yaudara da sata duk muna yi, kuma muna shirya kwas na musamman a kan wannan.”

Wannan ya kara tabbatar da cewa, Amurka za ta dauki duk matakin da ta ga dama don neman cimma burinta, kuma hakan ya kasance yadda take cudanya da kasa da kasa. (Mai Zane:Mustapha Bulama)

ShareTweetSendShare

MASU ALAKA

Xi Jinping Ya Tattauna Da Shugaban Koriya Ta Kudu Lee Jae-myung 
Daga Birnin Sin

Xi Jinping Ya Tattauna Da Shugaban Koriya Ta Kudu Lee Jae-myung 

November 1, 2025
Xi: A Hada Kai Wajen Gina Al’ummar Bai Daya Ta Asiya-Pasifik
Daga Birnin Sin

Xi: A Hada Kai Wajen Gina Al’ummar Bai Daya Ta Asiya-Pasifik

November 1, 2025
CMG Ta Kammala Gabatar Da Rahoto Kan Ganawar Shugabannin Sin Da Amurka
Daga Birnin Sin

CMG Ta Kammala Gabatar Da Rahoto Kan Ganawar Shugabannin Sin Da Amurka

October 31, 2025
Next Post
Tashar Samaniya Ta Sin: ‘Yan Sama Jannati Na Kumbon Shenzhou-14 Sun Fara Tattaki A Wajen Tashar

Tashar Samaniya Ta Sin: ‘Yan Sama Jannati Na Kumbon Shenzhou-14 Sun Fara Tattaki A Wajen Tashar

LABARAI MASU NASABA

Xi Jinping Ya Tattauna Da Shugaban Koriya Ta Kudu Lee Jae-myung 

Xi Jinping Ya Tattauna Da Shugaban Koriya Ta Kudu Lee Jae-myung 

November 1, 2025
Musabbabin Hana Sule Lamido Fom Ɗin Takarar Shugabancin PDP

Babban Burina Zama Fitacciyar Jaruma A Duniya —Aisha Umar

November 1, 2025
Xi: A Hada Kai Wajen Gina Al’ummar Bai Daya Ta Asiya-Pasifik

Xi: A Hada Kai Wajen Gina Al’ummar Bai Daya Ta Asiya-Pasifik

November 1, 2025
Dalibin Jami’ar Jos Ya Kashe Abokinsa Ya Binne Gawar A Rami

Dalibin Jami’ar Jos Ya Kashe Abokinsa Ya Binne Gawar A Rami

November 1, 2025
Sojoji Sun Kama Ƴan Ta’adda 20, Sun Ceto Mutane 17 Da Aka Yi Garkuwa Da Su

Sojoji Sun Kama Ƴan Ta’adda 20, Sun Ceto Mutane 17 Da Aka Yi Garkuwa Da Su

November 1, 2025
Waye Zai Lashe Ƙyautar Gwarzon Ɗan Wasan Afrika Na 2025?

Waye Zai Lashe Ƙyautar Gwarzon Ɗan Wasan Afrika Na 2025?

November 1, 2025
Gwamnatin Tarayya Ta Mayar Da Martani Kan Iƙirarin Trump Na Kisan Ƙare Dangi Ga Kiristoci

Gwamnatin Tarayya Ta Mayar Da Martani Kan Iƙirarin Trump Na Kisan Ƙare Dangi Ga Kiristoci

November 1, 2025
Shugabar Tanzania Samia Suluhu Ta Lashe Zaɓe, Duk Da Rikicin Da Ya Mamaye Ƙasar

Shugabar Tanzania Samia Suluhu Ta Lashe Zaɓe, Duk Da Rikicin Da Ya Mamaye Ƙasar

November 1, 2025
An Cafke Ma’aikatan Gidan Marayu Da Suka Sayar Da Yara 4 A Kan Naira Miliyan 3

An Cafke Ma’aikatan Gidan Marayu Da Suka Sayar Da Yara 4 A Kan Naira Miliyan 3

November 1, 2025
Musabbabin Hana Sule Lamido Fom Ɗin Takarar Shugabancin PDP

Yadda Gwamnatin Tarayya Ta Dakile Yaɗuwar Ɓarkewar Cutar Dabbobi A Jihar Jigawa

November 1, 2025

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.