Shugaban gudanarwar kungiyar kwallon kafa ta Barcelona, Juan Laporta, ya bayyana cewa kungiyar ta dawo hayyacin ta kuma zata ci gaba da kawo gyara domin samun nasara a wasannin dake gabanta a yanzu.
Laporta ya bayyana haka ne a kasar Saudiya bayan da kociyan kungiyar, Dabi Harnandez ya lashe kofinsa na farko a matsayinsa na kocin Barcelona bayan ya doke Real Madrid a wasan karshe na kofin Spanish Super Cup.
- Zaben 2023: Majalisar Dinkin Duniya Da ECOWAS Sun Yi Sabon Gargadi
- Ban Taba Jin Kunyar Sana’ar Sayar Da Maganin Mata Ba -Sahura Haruna
A wasan da aka buga a Saudiyya, dan was an gaba Gabi, mai shekaru 18 ne ya fara zura kwallon farko a ragar Real Madrid kafin Robert Lewandowski ya ci kwallo ta biyu sannan sai Pedri ya ci wa Barcelona kwallo ta uku kafin Karim Benzema ya farkewa Real madrid kwallo daya.
Barcelona ce ta fi haskakawa a wasan a yayin da Real Madrid na shiga cikin yanayi mara dadi a tsawon lokaci na was an kuma a yanzu haka Barcelona ce a saman teburin gasar La Liga inda ta baiwa Real Madrid tazarar maki uku.
Wannan shi ne wasa na takwas da kungiyoyin biyu suka kara a Spanish Super Cup, inda Real Madrid ta yi nasara a shida wato a (1988, 1990, 1993, 1997, 2012 da kuma 2017) ita kuwa Barcelona ta lashe a 2011 a wasan karshe da ta fuskanci Real Madrid a kofin.