Bata gari suma ‘ya’ya ne na wasu wadanda suka bar su ba wata tsawatawa ko sa masu sharuddan da za su taimaka masu zuwa Tudun mun tsira,sune wadanda za su iya bata Gida, Unguwa, Gari ,da abubuwan da basu da kyau wadanda kuma idan aka bari ana kallo hakanan abin ba zai haifar da da mai ido ba.
Suma suna da Iyaye kamar yadda kowa yake dasu, su kuma ne ya dace su kula dasu fiye da kowa, wasu dalilan sun hada da tashi hakanan babu mai kwabawa,hakan ta kan kasance ne ko dai ace sun rasa dukkan mahaifansu ya kuma zama babu wanda zai taimaka wajen tarbiyyarsu.
- Malam Ina So A Taimaka Mun Da Maganin Damuwa Da Bakin Ciki?
- Wani Abun Fashewa Ya Tarwatse A Wani Masallaci Ya Kashe Akalla Mutane 18 A Afganistan
Akwai‘ya’ya ko yara da suke da masu alhakin koyar dasu tarbiyyar ko yi masu duk abubuwan da za su rayuwarsu zata inganta a gaba.
Sai dai kashi! abin, takaici basu yin yadda yakamata hakanan suke barinsu kara-zube,masu iya magana sun ce da digon ruwa ake samu gulbi ya zama Kogi.
Irin wadannan ‘yaran ko ‘ya’yan da suke ba masu kulawa dasu kamar yadda nace wasu suna dasu, amma ba su abinda ya dace, abin yana iya zama matsala domin su duk abubuwan da suka yi babu mai ce masu uffan,neman yadda za su tafiyar da rayuwarsu suke.
Wasu na neman abinda abinda za su ci ne, wasu ba wurin kwanciya, wasu ba su zuwa makaranta, kai abubuwa dai masu yawa da suka kamata ace ana yi masu amma ba a yi.
Wanda ko wadanda suka ta shi babu masu sa,su yin abubuwan da suka kamata tun suna yara sune ke yi ma kansu duk abubuwan da suka kamata Iyaye ne suke, ko masu kulawa da su.
Idan har aka bar su hakanan sakaka babu tsawatawa watarana sai an yi dana- sani, sune kan tsinci kansu cikin gungun bata gari.